Bayani kan Sake Auren Maryam Sanda da yadda aka Nemi Buhari Ya Mata Afuwa
- Ana cigaba da magana kan afuwar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Maryam Sanda bayan kisan mijinta a 2017
- Mahaifin Maryam, Alhaji Sanda Garba ya ce ta tuba, kuma yanzu tana koyarwa a gidan gyaran halin da ake tsare da ita
- Mahaifin marigayi Bilyaminu, Ahmed Bello Isa ya ce ya yafe mata domin samun zaman lafiya da ceto rayuwar ’ya’yansu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Iyayen Maryam Sanda da marigayi Bilyaminu Bello sun bayyana jin daɗinsu da kuma godiya bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Maryam afuwa.
Maryam wacce aka yankewa hukuncin kisa a shekarar 2020 saboda laifin kashe mijinta da wuka a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2017, ta shafe shekaru tana zaman gyara hali kafin afuwar.

Source: Facebook
A wata hira da suka yi da tashar DW da aka wallafa a Facebook, iyayen sun bayyana cewa sun dade suna nema a fito da ita.
Tun bayan sanarwar afuwar, maganganun iyayen ɓangarorin biyu sun janyo martani daban-daban a kafafen sadarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maryam Sanda ta zama malama
Mahaifinta, Alhaji Sanda Garba, ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi babban aiki wajen ganin an saki diyarsa bayan dogon lokaci tana gidan gyaran hali.
Ya ce Maryam ta nuna alamun tuba da canji, domin yanzu haka tana koyarwa a cikin gidan gyaran hali, abin da ya nuna ta karɓi darasi daga abin da ya faru.
Garba ya ƙara da cewa mahaifin marigayi Bilyaminu Bello, Alhaji Ahmad Bello Isa, ya bayar da goyon baya wajen ganin an yi wa Maryam afuwa.
Batun yiwuwar aure bayan afuwa
Da aka tambayi Alhaji Sanda Garba kan yiwuwar auren diyarsa bayan ta dawo rayuwa ta yau da kullum, ya ce:

Kara karanta wannan
Atiku da fitattun 'yan Najeriya, kungiyoyi da jam'iyyu da suka yi adawa da afuwar Tinubu
“Sha’anin aure na Allah ne."
Bayan labarin afuwarta, Legit Hausa ta ga yadda wasu mutane suka fara hango zancen yiwuwar sake auren Maryam Sanda.
An nemi a Buhari ya saki Maryam Sanda
A nasa bangaren, mahaifin marigayi Bilyaminu Bello, Alhaji Ahmad Bello Isa, ya ce ya ji daɗin afuwar da aka yi wa Maryam domin ta samu damar renon yaran da Allah ya ba su.
Ya bayyana cewa tun lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nemi a sake ta amma ba a amince ba.
Alhaji Ahmad Bello Isa ya ce ya rubuta takardu da dama amma bai samu amsa daga gwamnatin Buhari ba.

Source: Facebook
“Na bar komai ga Allah,” Mahaifin Bilya
Da yake martani kan zargin cewa wasu ‘yan uwa sun yi adawa da yafiyarsa, mahaifin ya ce kowa yana da ‘yancin ra’ayinsa. Amma a matsayinsa na uba kuma musulmi, ya zabi yafiya.
Vanguard ta rahoto ya ce:

Kara karanta wannan
Hon. Farouk Lawan ya tabo batun rayuwa a gidan yari bayan Tinubu ya yi masa afuwa
“Ramuwa ba za ta dawo da ɗana ba, amma yafiya tana iya dawo da zaman lafiya ga iyalai da ’ya’yan da abin ya shafa.”
Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa
A wani labarin, mun rahoto muku cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa wasu fitattun mutane afuwa bayan samunsu da laifi.
Cikin wadanda shugaban kasar ya yi wa afuwa akwai wadanda aka kama da laifin kisan kai, garkuwa da mutane da safarar kwaya.
A kan haka Legit Hausa ta hada rahoto kan wasu fitattun mutane 6 da shugaban ya yi wa afuwa ciki har da Maryam Sanda da ta kashe mijinta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
