Ranar 'Yanci: Gwamnatin Tarayya Ta Bayar da Hutun Kwana 1 a Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Laraba mai zuwa, 1 ga watan Oktoba, 2025 a matsayin ranar hutu ga ma'aikata a fadin Najeriya
- Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya taya yan Najeriya murnar wannan rana
- A ranar 1 ga Oktoba, 2025, Najeriya za ta cika shekara 65 da samun 'yancin k ki kiai daga turawan mulkin mallaka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun ranar samun 'yancin kai, ranar da Najeriya ke cika shekaru 65 da samun yanci daga turawan mulkin mallaka.
Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025 a matsayin ranar hutu domin bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ’yancin kai.

Source: Twitter
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, shi ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Gwamna ya shiga rikicin Dangote da PENGASSAN, ya fadi abin kunyar da zai faru ga Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu ta taya yan Najeriya murna
Dr. Tunji-Ojo ya taya ’yan Najeriya da ke zaune a nan cikin gida da wadanda ke kasahaen waje murnar zagayowar wannan rana mai tarihi.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Magdalene Ajani ta rattaba wa hannu a ranar Litinin.
Minista Tunji-Ojo ya roƙi ’yan ƙasa da su ci gaba da rungumar kishin ƙasa, haɗin kai da juriya domin a cewarsa, wadannan ginshikar uku ke goye da Najeriya tun daga samun ’yancin kai a 1960 zuwa yau.
An ba da hutun ranar samun 'yancin kai
Sanarwar da ma’aikatar cikin gida ta wallafa a shafinta na X ta ce,
"Gwamnatin Tarayya ta ayyana Laraba, 1 ga Oktoba, 2025, a matsayin hutu na musamman domin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai.
“Mai girma Ministan Harkokin Cikin Gida, Hon. (Dr.) Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya yi wannan sanarwa a madadin Gwamnatin Tarayya, ya taya ‘yan Najeriya murnar wannan rana mai tarihi, a gida da waje.

Kara karanta wannan
Da sauran rina a kaba: Gwamna Abba ya yi maganar cikar Najeriya shekara 65 da 'yanci
“Dr. Tunji-Ojo ya shawarci ‘yan kasa da su ci gaba da nuna kishin kasa, hadin kai, da juriyar da ta karfafa al’ummar Najeriya tun daga samun ‘yancin kai a 1960. "

Source: Facebook
Tunji-Ojo ya kwantar da hankulan jama'a
Yayin da yake bayyana tabbacin cewa Najeriya za ta ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba, Ministan ya yi wa ‘yan kasa fatan yin bikin ranar yanci na bana cikin farin ciki.
Sanarwar ta ce:
“Tare da hadin kan ‘yan Najeriya baki daya, kasar za ta ci gaba da karfafa a zaman lafiya, da cigaban tattalin arziki. Ya yi wa ‘yan Najeriya fatan yin bikin yancin lai lafiya."
Gwamnatin Tinubu za ta gyara lantarki
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta yi ikirarin cewa nan ba da jimawa ba yan Najeriya za su ga an daina dauke wutar lantarki kwata-kwata.
Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka a Abuja yayin kaddamar da wasu ayyuka a Cibiyar Horas da Ma’aikatan Wutar Lantarki.
Adelabu ya ce wannan sababbin gine-gine sun shiga tarihi a cibiyar kuma za su taimaka wajen kara inganta bangaren makamashi a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng