Ana Maganar Sulhu, 'Yan Bindiga Sun Farmaki Motar Jami'an Tsaron NSCDC
- Rahotanni sun nuna cewa an kai hari kan jami’an NSCDC a hanyar Yantumaki–Danmusa a Katsina, inda aka kashe jami’i guda ɗaya
- Bayan farmakin, an gano cewa jami’ai huɗu sun samu raunuka, kuma an garzaya da su asibitin Dutsinma don samun kulawa
- Hakan na zuwa ne yayin da ake magana kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi da ‘yan bindiga a karamar hukumar Faskari
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina – A kalla jami’i guda ɗaya na hukumar tsaro ta NSCDC ya rasa ransa, yayin da wasu huɗu suka jikkata sakamakon harin kwanton bauna da ake zargin ‘yan bindiga suka kai musu.
Harin ya auku ne a garin Dafa da ke kan hanyar Yantumaki–Danmusa da misalin ƙarfe 5:00 na yamma.

Source: Twitter
Legit ta tattaro bayanai kan harin ne a cikin wani sako da mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X.

Kara karanta wannan
Sa'o'i da sulhu, 'yan bindiga sun rufe masallaci, sun sace masu sallah 40 da Asuba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamari ya tayar da hankali musamman ganin cewa lokaci ne da ake kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin wasu ‘yan bindiga da shugabannin al’umma a karamar hukumar Faskari.
Yadda 'yan bindiga suka kai wa NSCDC hari
Rahotanni sun tabbatar da cewa jami’an NSCDC sun fito ne daga wani aiki a lokacin da aka yi musu kwanton bauna.
Rahotanni sun bayyana cewa yayin harin, jami’i mai mukamin CCA, Adamu Abdullah, mai shekara 37, ya rasa ransa nan take.
Jami’an da suka jikkata sun haɗa da DSC Abdullah Usman, ASC Dikko Sabiu, ASC Haruna Bello, da CCA Kabir Dalhatu.
Matakin da aka dauka bayan harin
Bayan samun rahoton faruwar lamarin, jami’an tsaro daga garin Danmusa suka tura tawagar sintiri zuwa wurin domin bada agajin gaggawa.
An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Gwamnati na Dutsinma, inda ake ci gaba da kula da lafiyarsu.
Hakazalika, an kwato motar kirar Hilux da jami’an suka yi amfani da ita lokacin harin daga hannun ‘yan bindigar.
Masana sun ce lamarin ya sake tabbatar da barazanar da matsalar tsaro ke yi a Katsina, duk da yarjejeniyoyin zaman lafiya da ake kullawa da kungiyoyin ‘yan bindiga a yankunan jihar.
Yanayin tsaro a jihar Katsina
Jihar Katsina na daga cikin wuraren da rikicin ‘yan bindiga ya fi kamari a Arewacin Najeriya, inda ake fuskantar sace mutane, kisan gilla, da kuma hare-hare kan jami’an tsaro.
A karkashin haka ne gwamna Dikko Umaru Radda ya hada wani zama na musamman domin neman hanyar warware matsalar.

Source: Facebook
Hadimin gwamnan, Ibrahim Kalaha Muhammad ya wallafa a Facebook cewa taron ya hada masu rike da madafun iko a bangarori daban daban da suka fito daga jihar.
An sace mutum 40 a jihar Zamafara
A wani rahoton, kun ji cewa wasu da ake zargi 'yan bindiga ne sun kai hari wani masallaci a jihar Zamafara.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shiga wani masallaci ne ana sallar Asuba suka yi awon gaba da mutane.
Gwamnatin Zamfara da jami'an tsaro ba su yi karin haske ba game da harin da aka kai zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
