CCT: An Fadada Shirin Tallafin N25,000 duk Wata, Za a Dauki Karin Mutum 600,000 a Najeriya
- Gwamnatin tarayya za ta fadada shirin tallafawa magidanta masu karamin karfi na CCT bayan sama da mutane miliyan 5 sun amfana
- Karamin ministan harkokin jin kai, Dr. Yusuf Tanko Sununu ya ce za a kara daukar mutane 600,000 a fadin jihohin Najeriya
- A karkashin shirin CCT, kowane mai cin gajiya yana samun tallafin kudi N25,000 daga gwamnatin tarayya na tsawon watanni uku
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce fiye da magidanta miliyan 5.5 a Najeriya na ci gaba da amfana daga shirin Conditional Cash Transfer (CCT), wato tallafin kuɗi ga marasa ƙarfi.
Karamin Ministan Harkokin Jin Kai, Dr. Yusuf Tanko Sununu, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis, yayin ƙaddamar da Tsarin Kariya na ECOWAS da shirin aiwatar da shi a Abuja.

Source: Twitter
Gwamnatin Tinubu za ta fadada tallafin CCT
Ya ce gwamnati Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da shirin faɗaɗa wannan shiri domin kara daukar magidanta maza da mata 600,000 kafin ƙarshen 2025, in ji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dr. Sununu, wanda daraktan ci gaban zamani na ma’aikatar jin kai, Valentine Ezulu, ya wakilta, ya bayyana cewa shirin na daga cikin manufofin Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A tsarin shirin CCT, kowane mutum da aka dauka a karkashin shirin zai samu tallafin N25,000 duk wata daga gwamnatin Najeriya har na tsawon watanni uku
Yadda Tinubu ya kawo shirye-shiryen tallafi
Ministan ya ƙara da cewa hukumar kula da shirye-shiryen jin kai (NSIPA) ce ke jagorantar wannan aiki tare da wasu manyan shirye-shiryen gwamnati irin su GEEP, N-Power da sauransu.
A cewarsa, kirkirar tsarin rajistar magidanta masu rauni wanda yanzu ya ƙunshi bayanan mutane fiye da miliyan 19.7, ya taimaka wajen rabon tallafi ga waɗanda suka fi bukata.
Haka kuma ya ce gwamnati na tallafa wa kananan ‘yan kasuwa, maida 'yan gudun hijira gida, tare da horar da matasa su samu ƙwarewar zamani, The Nation ta kawo.
Za a kara daukar mutane 600,000 a shirin CCT
“A halin yanzu magidanta fiye da miliyan 5.5 ne ke amfana da shirin CCT, za mu fadada shirin domin daukar wasu 600,000 kafin ƙarshen shekara.
"Wannan tsarin zai tabbatar da cewa babu ɗan Najeriya da za a bari a baya, ko a cikin mawuyacin lokaci,” in ji shi.

Source: TikTok
Dr. Yusuf Sununu ya kara da cewa gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta wajen ganin ta ragewa yan kasa wahalhalu da kuncin rayuwar da ake ciki.
Wani da ya ci gajiyar shirin CCT, Ahmad Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa ya karbi N75,000 na watanni uku kuma ya ji dadin kudin.
A cewarsa, wannan tallafin yana da amfani amma magidanta sun fi bukatar saukar farashin kayayyaki domin su ne suke amfani da su yau da kullum.
"Ba laifi tallafin yana toshe wata matsalar amma ni abin da nafi bukata gwamnati ta yi shi ne farashi ya dawo yadda muka saba. Babu abin da ya fi damun magidanta kamar cefane.
"Kafin zuwan wannan gwamnatin nawa kayan masarufi suke? Nawa ake sayarwa yanzu? Ya jamata gwamnati ta duba," in ji shi.
Gwamnati za ta ba yan Najeriya 100,000 horo
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin horar da matasa 100,000 ayyuka tare da ba su takardar shaidar kwarewa a dukkan jihohin Najeriya.
An kaddamar da shirin ne ta hannun ma’aikatar gidaje da ci gaban birane a hadin gwiwa da kamfanin Polaris Capital.
Bayan horo da takardar shaidar aiki, za a hada kwararrun da aka horas da su da ayyuka kai tsaye ta hanyar amfani da wata sabuwar manhaja ta yanar gizo.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


