Ana Jimamin Hatsarin Jirgin Kasa, 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane a Kaduna
- 'Yan bindiga sun yi ta'asa bayan sun kai hare-hare a wasu kananan hukumomin jihar Kaduna guda biyu
- Miyagun 'yan bindigan sun hallaka mutane tare da raunata wasu daban bayan sun bude musu wuta
- Gwamnatin jihar Kaduna ta hannun kwamishinan yada labarai ta jajantawa mutanen da lamarin mara dadi ya ritsa da su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Mutane takwas sun rasa rayukansu, yayin da wasu takwas kuma suka samu raunuka sakamakon hare-haren da 'yan bindiga suka kai a jihar Kaduna.
'Yan bindigan sun kai hare-haren ne daban-daban a kananan hukumomin Kauru da Kudan na jihar Kaduna.

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta ce 'yan bindigan sun kai harin ne a kauyen Unguwan Rimi da ke masarautar Chawai a gundumar Kamaru ta karamar Hukumar Kauru, da kuma kauyen Ungwan Fulani da ke Hunkuyi a karamar hukumar Kudan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda 'yan bindiga suka kai hare-haren
Harin da aka kai a Kauru ya faru ne kusan shekaru biyu bayan da zaman lafiya ya dawo a Kudancin Kaduna, sakamakon tsarin zaman lafiya ba tare da amfani da karfi ba, wanda gwamnatin Gwamna Uba Sani ta aiwatar.
Shugaban kungiyar ci gaban Chawai, Abel Adamu, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa ‘yan bindigan sun mamaye kauyen Ungwan Rimi da safiyar Litinin, sannan suka fara harbe-harbe kan jama’a.
Abel Adamu ya yi ikirarin cewa maharan sun fito ne daga kauyen Maingo a karamar hukumar Bassa ta jihar Plateau, sakamakon rikicin da ya tashi a can, wanda daga bisani ya bazu zuwa Kauru a Kaduna.
Ya yaba da jajircewar Gwamna Uba Sani wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a Kudancin Kaduna cikin tsawon shekara biyu.
Sai dai ya roki hukumomin tsaro da su zurfafa bincike domin kamo masu hannu a harin tare da tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummomi, musamman na karkara waɗanda su ne mafi saurin fuskantar hare-hare.
Hakazalika, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Ungwan Fulani da ke karamar hukumar Kudan, inda suka harbe wani mutum mai shekaru 40 har lahira.
'Yan bindigan sun kuma yi garkuwa da wani ɗan kasuwa mai suna, Shehu Hussein, wanda yake da shekaru 53.
Gwamnatin Kaduna ta jajanta bayan harin
Gwamnatin jihar Kaduna ta hannun kwamishinan yada labarai, Ahmed Maiyaki, ta jajantawa iyalan waɗanda abin ya shafa.

Source: Facebook
Ahmed Maiyaki, ya bayyana harin a matsayin 'yan kadan waɗanda suka samo asali daga makwabtan jihohi masu iyaka da Kaduna.
Kwamishin ya ce jihar Kaduna ta kasance cikin kwanciyar hankali, sai dai hare-hare 'yan kaɗan da aka samu cikin shekaru biyu na mulkin Gwamna Uba Sani, sakamakon aiwatar da tsarin zaman lafiya.
'Yan bindiga sun kai hari a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.
'Yan bindigan sun yi garkuwa da mutum daya bayan sun kai hari a unguwar Zawachiki cikin dare.
Jami'an 'yan sanda sun garzaya zuwa wurin da lamarin ya auku bayan sun samu rahoton harin da 'yan bindigan suka kai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
