Mutuwar Mahaifiyar Shugaban APC Ta Girgiza Tinubu, Ya Aika da Sakon Ta'aziyya
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samu labarin rasuwar mahaifiyar shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda
- Mai girma Bola Tinubu ya nuna jimaminsa game da rasuwar Mama Lydia Yilwatda, wadda ta rasu a ranar Lahadi, 18 ga watan Agustan 2025
- Hakazalika, ita ma jam'iyyar APC reshen jihar Plateau ta aika da sakon ta'aziyyar ta kan rasuwar mahaifiyar Nentawe Yilwatda
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi alhini kan rasuwar mahaifiyar shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.
Shugaba Tinubu ya mika sakon ta’aziyyarsa ta musamman ga Farfesa Nentawe Yilwatda, bayan rasuwar mahaifiyarsa, Mama Lydia Yilwatda.

Source: Twitter
Mahaifiyar shugaban APC ta rasu
Ta'aziyyar shugaban kasan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanya a shafinsa na X, a ranar Litinin, 19 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan
'Abin da ya sa APC ta lashe mafi yawan zabukan cike gurbi da aka yi a Kano da jihohi 12'
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mama Lydia Yilwatda dai ta rasu ne da safiyar ranar Lahadi, 18 ga watan Agustan 2025, a asibitin koyarwa na jami’ar Jos.
Marigayiyar ta yi bankwana da duniya ne tana da shekaru 83.
Tinubu ya yi wa Nentawe ta'aziyya
Shugaba Tinubu ya bayyana marigayiyar a matsayin mace tagari wadda ta rayu cikin imani, hidima da kuma sadaukarwa ga al’ummarta.
"Shugaban kasa ya roki Farfesa Yilwatda da ya karɓi rasuwar mahaifiyarsa a matsayin ƙaddara daga Allah Maɗaukaki, tare da samun natsuwa duba da irin rayuwar da ta yi mai cike da manufa da kuma sadaukarwa."
"Shugaba Tinubu ya yi addu’a domin samun rahamar Allah ga Mama Yilwatda, tare da roƙon Ubangiji ya ba Farfesa Yilwatda, iyalansa baki ɗaya da duk wanda marigayiya ta bari hakurin jure wannan babban rashi."
- Bayo Onanuga
APC ta yi ta'aziyyar mutuwar Mama Lydia Nentawe
Hakazalika, jam’iyyar APC reshen jihar Plateau ta bayyana alhininta kan rasuwar mahaifiyar Farfesa Nentawe
APC ta yi ta'aziyyar ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin sakataren yaɗa labaranta, Shittu Bamaiyi, ya fitar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Source: Twitter
Jam’iyyar ta bayyana rasuwar a matsayin ba wai kawai babban rashi ne ga shugabanta ba, har ga dukkan 'ya'yan APC a jihar Plateau da kasar baki ɗaya.
Sanarwar ta bayyana cewa rasuwar ta kasance abin bakin ciki, musamman ga ‘ya’yanta, kasancewar ta rasu a wani lokaci da ake bukatar shawarwarin ta da addu’o’in ta a matsayin ta na uwa.
“Babu shakka, rasuwar marigayiya Mama ta kasance abin bakin ciki ga iyalan Yilwatda, domin ta rasu ne a lokacin da shawarwarin ta da addu’o’in ta suke da matuƙar muhimmanci, musamman ga shugaban jam’iyya na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda."
- Shittu Bamaiyi
Tinubu ya yabawa hukumar INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa hukumar zabe ta INEC kan yadda ta gudanar da zabukan cike gurbi.
Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa abin a yaba ne yadda aka gudanar da zabukan ba tare da wata fitina ko hargitsi ba.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar APC ta lallasa PDP a zaben cike gurbi na dan majalisar Jigawa da ya rasu
Hakazalika, ya taya murma ga dukkanin 'yan takarar da suka samu nasara a zabukan wadanda aka gudanar a mazabu 16.
Asali: Legit.ng
