'Ku Shirya': Abuja da Jihohin Arewa 14 Za Su Gamu da Ambaliyar Ruwa Ranar Juma'a

'Ku Shirya': Abuja da Jihohin Arewa 14 Za Su Gamu da Ambaliyar Ruwa Ranar Juma'a

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen ruwan sama da yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohin Arewa da Abuja ranar Juma’a, tana gargadin mazauna su dauki matakan kariya
  • NiMet ta hango ruwan sama da ambaliya a Abuja, jihohin Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da wasu jihohi a Kudu a ranar Juma’a
  • Hukumar ta shawarci hukumomi da kamfanonin jiragen sama su bi rahotannin yanayi, tare da shawarwarin daukar matakai don kare rayuka da dukiyoyi daga ambaliya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar NiMet ta shawarci mazauna babban birnin tarayya Abuja da wasu jihohin Arewa da su shirya wa ambaliyar ruwa a ranar Juma'a.

Wannan na kunshe ne a cikin hasashen yanayi na ranar Juma'a, 8 ga watan Agusta, 2025 da hukumar NiMet ta fitar.

Hukumar NiMet ta yi hasashen ruwan sama mai yawa da ambaliya a Abuja da jihohin Arewa 14
Hukumomin ceto na aikin ceto yayin da ambaliyar ruwa ta shiga wani gari. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

NiMet ta fitar da rahoton hasashen yanayin a sanarwar da ta fitar a shafinta na X a daren ranar Alhamis, 7 ga watan Agusta, 2025.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mummunar ambaliya a wurare 76 a Kano, Gombe da jihohi 17

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hasashen yanayi a jihohin Arewa

A safiyar ranar Juma'a, NiMet ta yi hasashen cewa ruwan sama marar karfi zai sauka a jihohin Sokoto, Kebbi, Katsina, Zamfara, Taraba, Kaduna, da Bauchi.

A yammacin ranar kuwa, ruwan sama na iya sauka a gaba daya jihohin da ke Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.

Sai dai, hukumar NiMet ta ce saboda karfin ruwan saman da zai sauka a ranar, akwai yiwuwar ambaliya ta afku a jihohin Kebbi, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa, Gombe, Bauchi, Adamawa da Taraba.

Hasashen yanayi a Arewa ta Tsakiya

Baya ga Arewa maso Yamma da Arewa maso Kudu, NiMet ta kuma yi hasashen saukar ruwan sama a babban birnin tarayya Abuja da jihohin Arewa ta Tsakiya.

A safiyar Juma'a, NiMet ta ce za a samu ruwa a sassan Abuja, Benue, Niger, Plateau, Kwara, Kogi, da kuma Nasarawa.

Amma a yammacin ranar, ana sa ran ruwan saman zai sauka ne a gaba daya jihohin da ke a wannan shiyya, hade da babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Za a sheka ruwan sama a Kano, Kaduna, NiMET ta hango ambaliya a jihohi 3

Harilayau, NiMet ta hango cewa za a samu ambaliyar ruwa a Abuja da jihohin Plateau, Benue, Niger, Kogi, da Nasarawa.

Hasashen yanayi a Kudancin Najeriya

Idan muka leka jihohin Kudancin kasar kuwa, hukumar NiMet ta ce za a samu ruwan sama a wasu sassan Ogun, Oyo, Osun, Ondo, Ekiti, Abia, Imo, Anambra, Ebonyi, Enugu, Akwa Ibom, Cross River, Lagos, da Edo a safiyar Juma'a.

Amma ana sa ran ruwa zai sauka ne a gaba daya jihohin Kudancin kasar a yammacin ranar ta Juma'a.

Ambaliyar ba ta tsaya a Arewa kadai ba, domin NiMet ta ce jihohin Kudu, irin su Lagos, Ogun, Oyo, Edo, Anambra, Imo, Rivers, Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River, da Delta za su gamu da ambaliya.

Ana fargabar cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya zai jawo ambaliya a Kudancin Najeriya
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya jawo ambaliya a cikin gari. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Shawarwarin NiMet ga 'yan Najeriya

Hukumar NiMet ta bukaci mazauna garuruwan da suka saba fuskantar ambaliyar ruwa da su gaggauta yin kaura ko su dauke matakan kare kawunansu.

NiMet ta kuma shawarci hukumomi, musamman na ba da agajin gaggawa da su zama a cikin shiri don kai dauki a inda za a iya samun ambaliya.

Kara karanta wannan

Ruwa zai yanke: NiMet ta saki sunayen jihohi 6 da za su fuskanci fari a Agusta

An kuma bukaci masu ruwa da tsaki, musamman kamfanonin jiragen sama da su samu rahotannin yanayi daga NiMet yayin shirya tafiye-tafiyensu.

Ambaliya za ta shafi Kano da jihohin Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Ma’aikatar Muhalli ta ƙasa ta yi gargaɗi game da yawan ruwa da ka iya haddasa ambaliya a fadin Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan an yi hasashen ruwan sama mai tsanani a wurare 76 da ke cikin jihohi 19 na Najeriya, ciki har da Kano.

Wani rahoto ya nuna cewa Gombe da Ogun sun riga sun fara fuskantar karin ruwa sama tun kafin lokacin hasashen ma'aikatar muhallin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com