Rana Ta Baci: Mota Ta Banke Barawo Lokacin da Ya Saci Babur a Masallaci
- Wani Abdullahi Kasolayo ya saci babur a masallaci lokacin da ake Sallah, amma wata mota ta kade shi yayin da yake ƙoƙarin tserewa
- Bayan samun mummunan rauni a kansa, wani mutumi ya kai Adullahi asibiti inda likitoci suka yi masa dinki a wurare biyu a kansa
- Rundunar ƴan sandan Kwara ta gurfanar da Abdullahi gaban kotu bisa tuhume tuhume uku da suka saba wa dokokin Penal Code
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Rana ta ɓaci ma wani barawon babur a jihar Kwara, yayin da mota ta yi ƙulin ƙulin Kubura da shi bayan ya tafka sata a masallaci.
Da ya ke yana da sauran shan ruwa a gaba, an ce likitoci sun yi masa dinki har a wurare biyu a kansa, sakamakon mummunan rauni da ya ji.

Asali: Twitter
An gurfanar da barawo gaban kotu a Kwara
Tun da fari, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wanda ake zargin, Abdullahi Kasolayo ya gurfana gaban kotun majistare ta kan zargin satar babur ana Sallah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin Abdullahi Kasolayo, ɗan shekara 36 da ke zaune a yankin Oko Olowo, Olorin, da laifuffuka uku da suka saba wa sashe na 342, 327 da 287 na Penal Code.
Tuhume tuhumen da ake yi wa Abdullahi, mai sana'ar birkilanci, sun hada da shiga wuri ba bisa ka'ida ba, barnata dukiya da kuma sata.
An garzaya da barawo asibiti a jihar Kwara
Wani Salman Tunde ne ya kai karar ga sashen yaki da garkuwa da mutane na hedkwatar 'yan sanda ta ilorin, cewa an sace babur dinsa kirar Bajaj.
Salman ya shaida wa 'yan sanda cewa an sace babur dinsa mai lambar inji DUZWEH57763 a kofar gidansa lokacin da zai shiga masallaci.
A cewar rahoton farko na rundunar 'yan sanda (FIR), an sace babur din ne kafin Salman Tunde ya fito daga masallaci.
Hukuncin da kotu ta yanke wa barawon
Rahoton 'yan sandan ya nuna cewa:
"Duk wani kokari na gano babur din ya ci tura har zuwa washe gari, 27 ga Maris, 2025, da misalin karfe 7:00 na safiya, lokacin da wani Taofeeq ya kira Salman ya ce ya ga babur din a yankin Oko-Olowo.
"Daga baya wanda ake zargin ya amsa laifinsa a lokacin da ake tuhumarsa, ya shaida cewa ya saci babur din kuma wata mota ce ta kade shi a kokarin tserewa da babur ɗin."

Asali: Original
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
"A cewarsa, wani bawan Allah ne ya hanzarta kai shi asibiti domin ceto rayuwarsa, inda ya sha dinkuna a kansa."
Adebayo Thomas ne jami'in da ya shigar da kara kan lamarin, yayin da Barista Toyin Onaolopo ya ke kare wanda ake zargin a kotu.
A hukuncin da ya yanke, alkalin kotun, N.T Ahmed ya ba da belin wanda ake zargin domin ba shi damar jinyar munanan raunukan da ya samu a kansa.
An kama barawon da ya rika a satar babur
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar ‘yan sanda ta jihar Sokoto ta bayyana kama wani shahararren ɓarawon babur da ake nema ruwa a jallo.
Wanda aka kama din, mai suna Kabiru Abubakar, ya shiga hannu ne bayan ya saci babur daga harabar wani asibiti da ke cikin birnin Sokoto.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, ASP Ahmad Rufa’i, ne ya shaida hakan ga manema labarai a ranar Laraba, 10 ga watan Yuli.
Asali: Legit.ng