Sun kama barawon babur a masallacin juma'a, sun banka masa wuta ya kone kurmus
- Abun takaici ya zama ruwan dare a Najeriya, inda manyan barayi suka zama abin sha'awa
- Kananan barayi kuwa, sai dai a kashe su a titi, kisan wulakanci
- Hukumomi basu fiye daukar wani mataki ba idan irin wannan ta faru
Wasu samari a jihar Zamfara, sun dauki hukunci a hannu, bayan da suka kama barawon babur a masallacin juma'a yayin da ake kokarin sauke faralli.
Sai dai, maimakon suyi daidai, sai suka yi ba daidai ba, inda suka lakadawa barawon duka, suka kuma banka mana wuta kamar yadda suka ga ana yi a kudanciin Najeriya.
Sai dai wannan lamari ya bakantawa jaama'a rai, ganin ba haka al'adar kasar Hausa ta saba yi ba, kuma ba haka doka ta tanada ba, musamman ma inda ake sharia ta addini.
DUBA WANNAN: Babu siyasa a takura Atiku ya biya gwamnati biliyoyi
Samari da 'yan mata masu tofa albarkacin bakinsu, sun bazama shafin sada zumunta na acebook, inda suke tofa albarkacin bakinsu, kan wannan lamari.
Wata budurwa, Sa'adat Soso, a shafinta ta facebook, inda ta nuna hoton gawar tahalikin, ta tsitsinewa masu wannan aika-aika, inda tace sam wannan ba tarbiyya bace, musamman ganin cewa akwai manyan barayin gwamnati da ke sata amma jama'a na sonsu da ma tallarsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng