An Yi Babban Rashi a Duniyar Musulunci, Sheikh Abduljalilu Nyandu Ya Rasu

An Yi Babban Rashi a Duniyar Musulunci, Sheikh Abduljalilu Nyandu Ya Rasu

  • Duniyar musulunci ta yi rashi da Allah ya yi wa shugaban mabiya aƙidar Ahlus-Sunnah an ƙasar Togo, Sheikh Abdul-Jalilu Nyandu rasuwa
  • Shugaban ƙungiyar JIBWIS da aka fi sani da Izala a Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya tabbatar da rasuwar babban malamin a wata sanarwa
  • Sheikh Bala Lau ya miƙa sakon ta'aziyya ga ƴan uwa da al'ummar musulman Togo da duniya baki ɗaya tare da addu'ar Allah Ya gafarta masa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Ahlus-Sunnah na ƙasar Togo, Sheikh Abdul-Jalilu Nyandu, ya riga mu gidan gaskiya.

Babban malamin wanda ya ba gudummuwa wajen karantar da musulmi da koyi da Sunnar Manzon Allah (S.A.W) ya rasu a ƴan kwanakin da suka gabata.

Bala Lau.
Sheikh Bala Lau ya yi ta'aziyyar rasuwar shugaban Ahlus-Sunnah na Togo, Sheikh Abdul-Jalilu Nyandu Hoto: Jibwis Nigeria
Asali: Facebook

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta Najeriya ta tabbatar da rasuwar malamin a wata sanarwa da ta wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Akwai wata a kasa: Kungiyar NCM ta gargadi 'yan Najeriya kan hadewar Atiku da El Rufai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

JIBWIS ta bayyana alhini da jimami kan rasuwar daya daga cikin fitattun malaman Afirka, wato shugaban Ahlus-Sunnah na ƙasar Togo, Sheikh Abdul-Jalilu Nyandu.

Sheikh Bala Lau ya yi ta'aziyyar Abduljalilu Nyandu

Shugaban JIBWIS na kasa, kuma shugaban haɗin kan ƙungiyoyin Ahlus-Sunnah na yammacin Afirka, Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau, ya miƙa sakon ta'aziyya.

Sheikh Bala Lau ya ce rasuwar Sheikh Nyandu babban rashi ne ba wai ga kasar Togo kadai ba, har ma da al’ummar Musulmi gaba ɗaya.

A cewarsa duba da irin gudummawar da ya bayar wajen yaɗa wa da karfafa akidar Ahlus-Sunnah a nahiyar Afirka, rasuwar shehin malamin babban rashi ne ga musulmi.

Sanarwar ta ce:

"Shugaban JIBWIS na Naijeriya, kuma shugaban haɗin kan ƙungiyoyin Ahlus-Sunnah na yammacin Afurka, Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau, na sanar da rasuwa tare da miƙa ta’aziyyar rasuwar shugaban Ahlus-sunnah na ƙasar Togo, Sheikh Abdul-Jalilu Nyandu."
Sheikh Bala Lau.
Shugaban Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi ta'aziyyar rasuwar Sheikh Abdul-Jalilu Nyandu Hoto: Sheikh Abdullahi Bala Lau
Asali: Facebook

'Allah Ya ji ƙan Sheikh Abdul-Jalilu Nyandu'

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya yi fallasa, ya fadi korafin jiga jigan APC kan Tinubu

Sheikh Bala Lau ya miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayin da al’ummar Musulmi ta ƙasar Togo, tare da rokon Allah Ya gafarta masa, Ya sanya kabarinsa cikin lambun Aljanna.

“Muna miƙa ta’aziyya ga ʼyan uwa da iyalai, al’ummar musulmin ƙasar Togo da duniyar musulmi baki ɗaya, bisa wannan babban rashi, Allah Ya masa rahama, Ya kyautata maƙwanci, Ya haɗa mu da shi a Aljannatul fir’dausi baki ɗaya” Inji Bala Lau.

Imam Bello ya rasu a jihar Kebbi

A wani labarin, kun ji cewa Imam Bello Jandutsi, ɗaya daga cikin malaman kungiyar Izala a jihar Kebbi ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayi Imam Bello ya kasance babban malami a Izala, kuma babban limamin masallacin Sheikh Abbas Jega da ke Rafin Atiku, a Birnin Kebbi da ke jihar Kebbi, inda ya shafe shekaru yana limanci.

Rahotanni sun taɓbatar da cewa an yi wa mrigayin sallar jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada a masallacin Sheikh Abbas Jega.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262