Najeriya Ta Yi Rashi: Tsohuwar Minista da Ta Kafa Tarihi Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
- Gwamna Dapo Abiodun ya nuna alhinin rasuwar Cif Adenike Ebun Oyagbola, mace ta farko da ta zama minista mai matsayi a majalisar tarayya a Najeriya.
- Gwamna Abiodun na jihar Ogun ya ce marigayiyar ta zama abin koyi ga mata a Afrika, tana da kwazo, jajircewa da kishin kasa, tare da neman daidaito a siyasa
- Ya yi addu’a Allah ya jikanta, ya kuma ba iyalanta hakurin jure wannan babban rashi da ya girgiza jihar Ogun da Najeriya baki daya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abeokuta, Ogun - Gwamnan Jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun, ya tura sakon ta'azziya ga iyalan marigayiya tsohuwar Minista a Najeriya.
Gwamna Abiodun ya nuna alhinin rasuwar Cif Adenike Ebun Oyagbola, mace ta farko da ta zama minista mai matsayi a Najeriya.

Kara karanta wannan
'Mulkin Fir'aunanci ake yi': Sule Lamido ya dura kan APC, ya roki alfarma a zaɓen 2027

Asali: Twitter
Tsohon sanata a Najeriya ya rasu
Jaridar Tribune ta tabbatar cewa marigayiyar Cif Oyagbola ta rasu tana da shekaru 94 a duniya a ranar Juma’a 28 ga watan Fabrairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kwanakin nan da suka gabata, Legit Hausa ta kawo rahoton cewa tsohon sanatan Ogun ta Yamma, Ayodeji Otegbola ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 91 a duniya.
Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai, ƴan uwa da abokan arzikin mamacin tare da addu'ar Allah ya ba su haƙuri.
Abiodun ya bayyana cewa mutuwar sanatan babban rashi ne ga jihar Ogun da ma Najeriya baki ɗaya, ya yi addu'ar Allah ya gafarta masa.
Mutuwar tsohuwar minista: Gwamna ya yi ta'azziya
Abiodun, cikin sakon ta’aziyyarsa a ranar Asabar, ya ce rayuwar marigayiyar ta nuna kwazo, jajircewa, tawali’u da kuma kishin hidima ga al’umma.
Gwamnan ya kara da cewa marigayiyar Iyalode ta yankin Yewa ta gina kyakkyawan turba da mata a Afrika za su iya bi don cimma daidaito a siyasa.

Kara karanta wannan
Ramadan: Tinubu ya tura sako ga Musulmi, ya yi albashir kan farashin abinci da fetur
Ya yi addu’a Allah ya jikanta, ya kuma ba iyalanta karfin gwiwa da hakurin jure wannan babban rashi da ba za a maye gurbinsa ba.

Asali: Facebook
Gwamna ya yi addu'o'i ga marigayiya Oyagbola
A cikin sanarwar, Abiodun ya ce:
“Ina mika ta’aziyyata ga mutane da iyalan Akinola na Igan-alade a Karamar Hukumar Yewa ta Arewa kan rasuwar wannan fitacciyar ’ya ta Jihar Ogun.
“Muna godiya ga Allah bisa rayuwarta mai albarka da irin gudunmawar da ta bayar a fagen siyasa da kuma matsayin jakadiya mai kima.
“Allah ya jikanta, ya kuma kare iyalanta daga duk wani abu da zai girgiza su."
Sarkin Sasa da ke Ibadan ya rasu
Kun ji cewa al'ummar Hausawa sun shiga alhini bayan sanar da rasuwar fitaccen basarake a Najeriya da ya shafe shekaru 125 a duniya.
Rahotanni sun tabbatar Allah ya yi wa Sarkin Sasa da ke Ibadan a jihar Oyo, Alhaji Haruna Maiyasin rasuwa bayan ya shafe shekaru da dama kan karagar sarauta.
An ce marigayin kafin rasuwarsa, shi ne ke riƙe da muƙamin Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a jihohi 17 na Kudu.
Asali: Legit.ng