"Abin Kunya ne ga Najeriya," Gwamna Bala Ya Yi Magana Mai Zafi kan Karancin Abinci

"Abin Kunya ne ga Najeriya," Gwamna Bala Ya Yi Magana Mai Zafi kan Karancin Abinci

  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce abin kunya ne kasa kamar Najeriya ta gaza samar da wadataccen abinci ga ƴan ƙasa
  • Sanata Bala ya bayyana cewa Najeriya na da mutane sama da miliyan 250 kuma tana da ɗumbin albarkatun da za ta ciyar da su
  • Gwamnan ya yi wannan furuci ne yayin da ya karɓi bakuncin jakadan kasar Portugal a Najeriya a fadar gwamnatinsa da ke Bauchi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya nuna damuwa kan gazawar Najeriya wajen cimma wadatar abinci duk da dimbin albarkatun da take da su.

Bala Mohammed, Kauran Bauchi ya ce abin kunya ne ga kasa mai yawan jama’a sama da miliyan 250 ta kasa ciyar da ‘yan kasarta yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Gombe ta fusata, an ba da umarnin farauto makasan malamin addini

Gwamna Bala Mohammed.
Gwamnan Bauchi ya ce bai kamata Najeriya ta gaza wadatar da abinci ga ƴan kasa ba Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Gwamnan ya yi wannan bayani ne jiya a fadar gwamnatinsa yayin da ya karbi bakuncin jakadan Portugal a Najeriya, Paulo Martins Santos, Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jakadan ya gana da Gwamna Bala a wata ziyara ta ban girma da ya kai jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ƙarancin abinci abin kunya ne ga Najeriya

Da yake jawabi, Gwamna Bala ya ce:

“Ko da mutum yana aikin gona, kasuwa tana nan. Muna da ‘yan Najeriya miliyan 250, amma abin kunya ne cewa har yanzu ba mu iya ciyar da kanmu.
"Idan ba za mu iya samar da isasshen abinci ba, to mu sani ba mu hau kan tafarkin ci gaba ba, kuma ba za mu iya bunkasa ta kowace hanya ba."

Bauchi ta shirya ba masu zuba jari dama

Ya ce Bauchi na da filayen noma masu fadin hekta miliyan hudu, kuma ya tabbatar wa masu zuba jari daga Portugal cewa za su samu cikakkiyar dama ba tare da matsalolin tsarin mulki, cin hanci, ko haraji mai yawa ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ɗaga darajar addinin Musulunci da ya buɗe babban masallacin Juma'a

“A shirye muke mu karbi masu zuba jari daga Portugal don su yi noma, su fitar da kayayyaki, su samar da ayyukan yi, kuma su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki tare da karancin haraji da babu cin hanci,” in ji shi.

Gwamnan ya yi nuni da damar da ke akwai wajen yin hadin gwiwa tsakanin Bauchi da Portugal, yana mai jaddada irin arzikin da jihar ke da shi.

“Muna da dimbin albarkatun kasa da suka hada da ƙarfe, zinariya, dutsen ƙarfe da duk wani nau’in albarkatu da za a iya tunani."

Gwamna Bala ya yabawa kasar Portugal

Gwamna Bala ya yabawa Portugal bisa kyakkyawar alaka da Najeriya, yana mai nuna farin cikinsa da yiwuwar ƙarfafa haɗin gwiwa.

Gwamnan Bauchi ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki da jawo hannun jari daga ƙasashen waje.

Ya tabbatar wa jakadan cewa ƙofar jihar Bauchi a bude take don zuba jari a bangarorin da suka hada da yawon bude ido, noma, kiwon lafiya, ilimi, makamashi, kasuwanci da masana’antu.

Kara karanta wannan

Rusau: Abba zai kashe biliyoyi wajen yin asibiti, tituna, lantarki a Rimin Zakara

Gwamnatin Bauchi ya caccaki Yusuf Tuggar

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Bauchi ya soki ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar bisa kalaman da ya yi kan Gwamna Bala Mohammed.

Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Bauchi, Aminu Hassan Gamawa ya zargi ministan da gazawa a muƙamin da shugaban ƙasa ya ba shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262