Ana Zargin Tsohon Ministan Najeriya da Yin Lalata da Budurwa, Kotu Ta Yi Hukunci
- Kotun Majistare a Abuja ta bayar da belin tsohon minista, Kabiru Turaki, SAN, akan N1m bayan zarginsa da yin lalata da wata budurwa
- Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon ministan ayyuka na musamman kan zargin ya yi zaman auren bogi da wata Hadiza Musa Bafta
- Mai shari’a Abubakar Jega ya dage karar zuwa 11 ga Maris bayan da Kabiru Turaki ya karyata dukkan zarge-zargen da EFCC ke yi masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kotun Majistare ta Babban Birnin Tarayya ta bayar da belin tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Turaki, SAN, kan N1m.
An zargi Turaki da yin auren karya, lalata, da sauran laifuka masu nasaba da haka, wadanda suk ya musanta su da aka karanta masa a ranar Alhamis.

Asali: Twitter
Ana zargin Turaki da aikata laifuffuka 3

Kara karanta wannan
Girma ya fadi: An sake gurfanar da tsohon minista a kotu kan zargin dirka wa yarinya ciki
'Yan sanda sun fara gudanar da bincike bayan wani korafi da aka gabatar a ranar 9 ga Agusta, 2024, kafin suka gurfanar da shi a kotun, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan mai gabatar da kara ya ce an zargi Turaki da yin auren karya, zina da barazana, laifukan da suka saba wa sashe na 383, 387, da 389 na Kundin Laifuka.
Rahoton farko ya nuna cewa Turaki ya yi zaman auren karya da Hadiza Musa Bafta a wani otal da ake kira Han’s Place daga Disamba 2014 zuwa Agusta 2016.
Zarge-zargen da ake yiwa tsohon ministan
Rahoton ya ci gaba da cewa:
"Ya ci gaba da zaman dadiro da ita a Ideal Home Holiday, Asokoro, daga Agusta 2016 zuwa Nuwamba 2021, inda ya yi mata karyar cewa zaman aure suke yi.
"Turaki ya kama mata gida a Guzape cikin Nuwamba 2021, inda ya ci gaba da saduwa da ita da sunan ya aure ta har suka haifi diya mace."

Kara karanta wannan
Kotu za ta yanke hukunci kan shari'ar mabarata da Minista bayan korafin Abba Hikima
Rahoto ya ce tsohon ministan ya tsallake ya bar matar da diyarta, ya kuma musanta cewa shi ne mahaifin yarinyar tare da yin barazanar amfani da matsayinsa don cutar da su.
Kotu ta yanke hukunci kan ba da belin Turaki
The Nation ta rahoto mai gabatar da kara, Chijioke Okorie, ya nemi a saka ranar shari’a bayan Turaki ya musanta aikata dukkanin laifuffukan da aka karanta masa.
Lauyan Turaki, A. I. Mohammed, bai yi gardama ba kan sanya ranar shari’a amma ya roki kotu ta bayar da beli, yana mai tabbatar da cewa Turaki zai halarci zaman kotun.
Mai shari’a Abubakar Jega ya bayar da belin Turaki akan N1m tare kawo masu tsaya masa mutum biyu, wadanda za su nuna shaidar cewa su mazauna yankin ne.
Ana zargin tsohon sanata da lalata da budurwa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Ishaku Abbo daga jihar Adamawa ya sake jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta bayan bayyanar wani sabon bidiyo.

Kara karanta wannan
Dambarwar Albany da abubuwa 4 da suka ta da kura a kafofin sadarwa a Arewacin Najeriya
A bidiyon, an ga wani mutum da ake zargin shi ne Sanata Abbo yana lalata da wata mata da ake zargin matar aure ce.
Sai dai Sanata Abbo ya musanta zargin, yana mai cewa ba shi ba ne mutumin da ke cikin bidiyon, ba tare da karin bayani ba.
Asali: Legit.ng