Sanatan NNPP Ya Kwararo Yabo ga Tinubu kan Wani Muhimmin Aiki a Kano

Sanatan NNPP Ya Kwararo Yabo ga Tinubu kan Wani Muhimmin Aiki a Kano

  • Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu ya ji daɗin amincewa da ƙudirin dokar kafa kwalejin kimiyya da fasaha a jihar Kano
  • Kawu Sumaila na jam'iyyar NNPP ya yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan rattaɓa hannu a ƙudirin domin ya zama doka
  • Fitaccen 'dan adawan a majalisa ya bayyana cewa kafa kwalejin zai kawo ci gaba ba a Kano kaɗai ba, har da ma Najeriya baki ɗaya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Kawu Sumaila, na jam'iyyar NNPP, ya yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Kawu Sumaila ya yabi shugaba Tinubu ne kan rattaɓa hannu a kan ƙudirin dokar kafa kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya, Rano, a jihar Kano.

Kawu Sumaila ya yabawa Tinubu
Kawu Sumaila ya yabi Shugaba Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Sen. Abdulrahman Kawu Sumaila
Source: Facebook

Sanata Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Abuja a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

'Yan APC sun nunawa Kwankwaso yatsa kan batun komawa jam'iyyar

Meyasa Kawu Sumaila ya yabi Tinubu?

Kawu Sumaila ya bayyana cewa amincewar da Tinubu ya yi domin kafa kwalejin zai inganta ilmin sana’o’i a Kano da ma fadin ƙasar nan baki ɗaya.

"Kafa wannan makarantar ba wai nasara ce ga yankinmu kaɗai ba, wata babbar dama ce da za ta kawo sauyi ga jihar Kano da ma Najeriya gaba ɗaya."
“Za ta ba matasanmu damar samun ingantaccen ilmin sana’o’i da fasaha tare da samar musu ƙwarewa da dabarun da za su taimaka musu su yi fice."

- Sanata Kawu Sumaila

Sanata Kawu Sumaila ya yabi ɗan majalisa

Haka zalika, Kawu Sumaila ya yabawa wanda ya gabatar da ƙudirin dokar, Hon. Kabiru Rurum, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Rano/Bunkure/Kibiya, saboda jajircewarsa da hangen nesansa wajen tabbatar da nasarar ƙudirin.

“Ina kuma miƙa godiya ta ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ki amincewa da kafa sabuwar jami'a a Arewa, ya fadi dalili

“Haka nan, ina kuma jinjinawa shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas , da sauran ƴan majalisar tarayya baki ɗaya bisa haɗin kansu wajen tabbatar da amincewa da wannan ƙudirin"

- Sanata Kawu Sumaila

Sanatan NNPP ya shawarci gwamnatin Kano

Sanata Kawu ya buƙaci gwamnatin jihar Kano da ɗaukacin al’ummar jihar da su goyi bayan wannan muhimmin aikin ci gaban da aka kawo.

“Muna buƙatar haɗin kan kowa da kowa domin gina makoma mai kyau ga Kano ta Kudu, jihar Kano, da Najeriya baki ɗaya, a bisa kudirin ‘Renewed Hope Agenda’ na shugaba Tinubu."

- Sanata Kawu Sumaila

Shugaba Tinubu zai ziyarci Faransa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Najeriya domin ziyartar birnin Paris na ƙasar Faransa.

Shugaba Tinubu zai ziyarci birnin ne domin wata ziyara ta ƙashin kansa kamar yadda na kusa da shi suka bayyana a cikin wata sanarwa.

A yayin ziyarar ta sa, Tinubu zai gana da Shugaba Emmanuel Macron na ƙasar Faransa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng