Yadda Jihar Kaduna Ta Kafa Tarihin Jagorantar Najeriya a Noman Inabi

Yadda Jihar Kaduna Ta Kafa Tarihin Jagorantar Najeriya a Noman Inabi

  • Shugaban Ƙungiyar Manoman Inabi ta Ƙasa, Abdullah Dalhatu, ya bayyana cewa Kaduna ita ce babbar mai samar da inabi a Najeriya
  • Rahotanni sun nuna cewa karamar hukumar Kudan kadai tana samar da kusan kashi 85% na inabin da ake nomawa a kasar nan
  • Wata gonar inabi a Kudan ta samar da tan 22 na inabi a watan Janairu kadai, wanda aka fitar zuwa sassan Najeriya daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Shugaban kungiyar manoman Inabi ta kasa, Abdullah Dalhatu, ya ce jihar Kaduna, musamman a Ƙaramar Hukumar Kudan, ita ce ke da babbar damar samar da inabi a Najeriya.

Ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da ya jagoranta tare da shugaban karamar hukumar Kudan, Dauda Iliya Abba, zuwa gonar inabi mai girman kadada biyar a yankin.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Inabi
Kaduna ta zama kan gaba wajen noma inabi a Najeriya. Hoto: Kudan Local Government
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda ake nomar inabi a jihar Kaduna ne a cikin wani sako da shafin karamar hukumar Kudan ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi Dalhatu ya bayyana cewa gonar ta samar da tan 22 na inabi a watan Janairu na wannan shekara kadai.

Ya kara da cewa yanayi mai kyau da kasa mai kyau a Arewacin Najeriya, musamman a Kudan, sun zama ginshikan nasarar noma inabi a yankin.

Kaduna ta zama jagorar noma inabi

A cewar Abdullah Dalhatu, gonakin inabi a Kudan suna da damar samar da nau’ikan inabi masu yawa, wanda ke da tsawon rai har na shekaru 50.

Abdullahi Dalhatu ya bayyana cewa;

“Daga shekara ta farko, kowane reshe zai iya samar da kilogram 15 na inabi, sannan wannan yawan yana karuwa zuwa kilogram 85 daga bisani,”

Ya kara da cewa inabin da ake nomawa a yankin na da tsawon rai da ke kaiwa tsawon kwanaki 45 zuwa 50 ba tare da ya lalace ba idan aka adana shi cikin yanayi mai kyau.

Kara karanta wannan

"Ya karya doka," An tsige ɗan Majalisar APC daga kujararsa, INEC za ta canza zaɓe

Gudummawar Kudan wajen samar da inabi

Ƙaramar hukumar Kudan tana samar da kashi 85% na inabin da ake noma a Najeriya, wanda ake rarrabawa zuwa sassa daban-daban na ƙasar nan.

Shugaban karamar hukumar Kudan, Dauda Iliya Abba, ya yaba wa jajircewar manoman yankin wajen zama gaba da sauran sassa a harkar noma inabi.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa shugaban karamar hukumar ya ce;

“Noma a Jihar Kaduna yana da matuƙar tasiri wajen habaka tattalin arziki da bunƙasa yankuna, musamman a karamar hukumar Kudan.”

Martanin jama’a kan noma inabi a Arewa

A kafafen sada zumunta, mutane da dama sun bayyana jin daɗinsu da wannan cigaban a Arewacin Najeriya..

Abubakar Ahmad Usamatu ya rubuta cewa:

“Masha Allah. Ya kamata mu farka sosai, musamman mu 'yan Arewa. Noma ita ce ginshiƙin rayuwarmu kafin zuwan man fetur."

Kara karanta wannan

Abubuwan da 'yan Najeriya suka fada bayan Buhari ya yi kyautar daloli

"Muna addu’a Allah ya daukaka yankinmu da Najeriya baki ɗaya.”

Sauran masu sharhi sun yaba da cigaban, suna mai bayyana cewa noma inabi zai zama babbar hanyar samun kuɗin shiga ga manoma da gwamnati idan aka mayar da hankali a kansa.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Kudan ya tabbatar da cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, yana da shirin tallafawa noma a jihar domin tabbatar da cigaban tattalin arziki.

Ana shirin bunkasa noma a Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa na shirin bunkasa aikin noman zamani ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Gwamna Umar Namadi ya ziyarci kasar China domin yarjejeniya da wani kamfani da zai horar da 'yan jihar Jigawa noman zamani domin habaka tattali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng