Jami'ar Nijar: Jami'a ta sanya wa titi sunan marigayiya Hanifa Abubakar

Jami'ar Nijar: Jami'a ta sanya wa titi sunan marigayiya Hanifa Abubakar

  • Jami'ar Maryam Abacha da ke jamhuriyar ta sanya wa wani titi a cikin jami'ar sunan marigayiya Hanifa
  • Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan gano wani makashi ya hallaka Hanifa bayan sace ta da kwanaki
  • A wasu hotunan da muka samo, an ga wasu jami'an jami'a na kaddamar da titinn, inda aka rubuta 'HANEEFA ABUBAKAR ABDULSALAM STREET"

Jamhuriyar Nijar - Wata jami'a a jamhuriyar Nijar, Maryam Abacha American University ta sanyawa wani titi sunan Hanifa Abubakar Abdulsalam.

Hanifa Abubakar, wata yarinya mai shekaru 5, an yi mata kisan gilla a jihar Kano, bayan da wani malami kuma shugaban makaranta ya sace ta.

Jami'ar Nijar: Jami'a ta sanya wa titi sunan marigayiya Hanifa Abubakar
Jami'ar Nijar: Jami'a ta sanya wa titi sunan marigayiya Hanifa Abubakar | Hotuna: Arewa Media
Asali: Facebook

Bayan kisan Hanifa, jama'a da dama sun damu matuka kan labarin, lamarin da ya kai ga tsoma baki daga gwamnatin Kano da ma na Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun ceto tsohon kansilan da yan bindiga suka sace a Nasarawa

A wasu hotunan da Legit.ng Hausa ta samo a shafin Arewa , an ga wasu jami'an jami'ar na jikin allon da titin da aka sanyawa suna 'HANEEFA ABUBAKAR ABDULSALAM'

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli hotunan a kasa:

Jami'ar Nijar: Jami'a ta sanya wa titi sunan marigayiya Hanifa Abubakar
Jami'ar Nijar: Jami'a ta sanya wa titi sunan marigayiya Hanifa Abubakar | Hotuna: Arewa Media
Asali: Facebook

Jami'ar Nijar: Jami'a ta sanya wa titi sunan marigayiya Hanifa Abubakar
Jami'ar Nijar: Jami'a ta sanya wa titi sunan marigayiya Hanifa Abubakar | Hotuna: Arewa Media
Asali: Facebook

An kamo matar makashin Hanifa, an kai ta kotu, amma ta musanta komai

A wani labarin, Jamila Muhammad Sani, matar makashin Hanifa Abubakar ‘yar shekara 5, ta gurfana a gaban babban kotun majistare na jihar Kano da ke zama a Gidan Murtala, Kano, bisa zargin hannu a boye Hanifa.

Jamila, ‘yar shekara 30, matar Abdulmalik Tanko ce, wanda ake shari’a kan tuhume-tuhume hudu da suka hada boye wacce aka yi garkuwa da ita, hada baki, garkuwa da dan mutum da kuma kisan kai.

Mai gabatar da kara, a yayin da take karantawa Jamila rahoton farko na bayanai, ta yi zargin cewa ta boye wacce aka sace a gidanta na tsawon kwanaki biyar.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: EFCC ta damke babban jigon APC kan almundahanar N1.3bn

Asali: Legit.ng

Online view pixel