'Yan Bindiga Sun Shiga Wurin Ibada, Sun Kashe Malamin Addini Har Lahira
- An shiga jimami s ƙaramar hukumar Ipokia ta jihar Ogun da ke yankin Kuɗu maso Yammacin Nsaeriya bayan ƴan bindiga sun kai hari a coci
- Ƴan bindigan ɗauke da bindigog ƙirar AK-47 sun kutsa kai cikin wurin ibadar inda suka hallaka limamin cocin mai suna Yoni Adetula
- Majiyoyi sun bayyana cewa marigayin wanda kwamandan wata rundunar tsaro ne ya daɗe yana takun saƙa da masu fasa ƙwauri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ogun - Ƴan bindiga sun kai hari a cocin Celestial Church of Christ (CCC) da ke garin Idiroko a ƙaramar hukumar Ipokia ta jihar Ogun.
Ƴan bindigan a yayin harin sun bindige limamin cocin, Yomi Adetula, har lahira yayin da yake wa’azi a ranar Lahadi.

Asali: Original
Jaridar Leadership ta ce wani ganau ba jiyau ba ya tabbatar da aukuwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindiga suka kashe malamin addini
Ya bayyana cewa maharan waɗanda sun kai kimanin mutum shida, ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 sun yi basaja ne bayan sun sanya tufafin Cocin Celestial.
Shaidar ya bayyana cewa maharan sun shiga cocin da ke yankin Odo Eran a kan hanyar Old Garrage a Idiroko, inda suka buɗewa limamin wuta har ya mutu.
Har ila yau, maharan sai da suka tabbatar da mutuwarsa sannan suka yi gunduwa-gunduwa da gawarsa kafin su bar wurin.
Bayanai sun nuna cewa marigayin shi ne kwamandan rundunar So-SAFE Corps na yankin Idiroko, wacce gwamnatin jihar Ogun ta kafa da nufin kare jama’a daga barazanar ƴan ta’adda.
Ko da yake ba a gano dalilan da ya sanya aka kashe shi ba, majiyoyi sun bayyana cewa Yomi Adetula ya daɗe yana takun saƙa da wata ƙungiyar masu fasa-kwauri a garin Idiroko. Hakan ya sa aka tura shi zuwa Abuja a watan Disamba na 2024.
Haka kuma, wasu majiyoyi daga cocinsa sun bayyana cewa wannan takun saƙar ya sanya wasu masu fasa-ƙwauri suka rufe cocinsa da ƙarfin tsiya a watan Disamba.
Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin
Kwamandan rundunar So-SAFE Corps na jihar, Soji Ganzalo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce labarin mutuwar ya sanya shi cikin baƙin ciki.
Soji Ganzalo ya kuma ba da tabbacin cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai an gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Ya ƙara da cewa za su bai wa hukumomin tsaro bayanai masu muhimmanci don gano waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi.
Jami'an tsaro sun daƙile harin ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun nuna bajinta yayin da suka samu nasarar daƙile wani hari da ƴan bindiga suka kai a jihar Katsina.
Jami'an tsaron da suka haɗa da sojoji, ƴan sanda da DSS sun yi nasarar sheƙe ƴan bindiga guda bakwai bayan sun yi musayar wuta.
Sun kuma samu nasarar ƙwato dabbobi masu yawa waɗanda ƴan bindigan suka sace a harin da suka kai.
Asali: Legit.ng