Gwamnan Kaduna Ya ba Ƴan Bindiga Kuɗi Domin Su Tuba? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamnan Kaduna Ya ba Ƴan Bindiga Kuɗi Domin Su Tuba? Gaskiya Ta Bayyana

  • Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya tabbatar da cewa ko kwandala ba su ba ƴan bindiga da nufin su ajiye makamai ba
  • Malam Uba Sani ya share wannan tantama ne kwana ɗaya tal bayan gwamnatin Kaduma ta karɓi rukunin farko na tubabbun ƴan bindiga
  • Gwamnatin ta kuma buɗe wata kasuwar shanu da ta shafe shekaru 10 a rufe saboda matsalar tsaro a ƙaramar hukumar Birnin Gwari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya ce ba su ba ƴan bindiga ko Naira da nufin su tuba su ajiye maƙamai ba.

Uba Sani ya kuma yi fatali da raɗe-raɗin da ake cewa gwamnatinsa na iya zaman sulhu da tubabbun ƴan bindiga domin a samu zaman lafiya.

Gwamnan Kaduna, Uba Sani.
Gwamnan Kaduna ya ce ko Naira ba a ba ƴan bindigar da suka miƙa wuya ba Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne da yake jawabi a wata hira da gidan talabijin na Channels tv a shirin siyasa a yau.

Kara karanta wannan

"Mutane sun zama mabarata," Jigon APC ya koka kan tsadar kayan abinci a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Kaduna ya karɓi tubabbun miyagu

Wannan hira na zuwa ne sa'o'i 24 bayan gwamnatin Kaduna ta karɓi wasu ƴan bindiga da suka tuba suka ajiye makamansu.

Da aka tambaye shi ko gwamnatin Kaduna ta cakewa ƴan bindigar wasu kuɗaɗe kafin su amince da miƙa wuya, Malam Uba Sani ya ce:

"Ba mu ba su ko Naira ɗaya ba, babu batun da ya shafi kuɗi a lamarin gaba ɗaya, galibinsu da ma sun gaji.
"Abin da muka yi mun zaunar da su, muka tambaye su meyasa kuka zaɓi zama a jeji, kuna farmakar mutane kuna sace su?"

A ranar Alhamis da ta gabata, gwamnatin jihar Kaduna karkashin Malam Uba Sani ta karbi rukunin farko na tubabbun ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Birnin-Gwari.

Uba Sani ya buɗe kasuwa bayan shekara 10

Gwamnatin ta kuma buɗe kasuwar shanu, wacce aka rufe kusan shekaru 10 da suka wuce saboda matsalar tsaron da ta addabi yankin.

Kara karanta wannan

"Babu wanda zai canza yin Allah," Gwamna ya faɗi saƙon da ake turo masa a waya

Sao dai a yanzu, Malam Uba Sani ya ce ko Naira ba su ba wani ɗan bindiga domin jawo ra'ayinsa ya ajiye makamai, rahoton Daily Trust.

Yan bindiga sun nemi fansar N300m a Kaduna

Ku na da labarin ƴan bindigan da suka sace wasu yara a Kaduna sun tuntuɓi mahaifinsu domin ya ba su kuɗin fansa kafin su sake shaƙar iskar ƴanci.

Hatsabiban ƴan bindigan sun buƙaci a ba su N300m a matsayin kuɗin fansa kafin su saki yaran da aka dauke a ƙaramar hukumar Chikun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262