Kaduna: Gwamna Uba Sani Ya Karbi Kasurguman Yan Bindiga da Suka Tuba

Kaduna: Gwamna Uba Sani Ya Karbi Kasurguman Yan Bindiga da Suka Tuba

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta karbi wasu kasurguman yan bindiga da suka ajiye makamansu kan ayyukan ta'addanci
  • Gwamnan jihar, Uba Sani shi ya karbi tababbun yan bindigar inda ya dauka musu alkawuran samar da zaman lafiya
  • Hakan na zuwa ne yayin da jihar musamman yankunan karkara ke fama da hare-haren yan bindiga a tsawon shekaru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Wasu daga cikin manyan yan bindiga da dama a jihar Kaduna sun ajiye makamansu.

Gwamna Uba Sani shi ya karbi sababbin tuban a yau Alhamis 28 ga watan Nuwambar 2024 a jihar.

Kasurguman yan bindiga sun tuba a Kaduna
Gwamna Uba Sani ya karbi tubabbun yan bindiga a jihar Kaduna. Hoto: Uba Sani.
Asali: Twitter

Gwamna Uba ya bude kasuwa da ta dade a kulle

Tribune ta tabbatar da cewa bayan karbar yan bindigar, Uba Sani ya bude wata kasuwa da ta shafe shekaru 10 a kulle saboda rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 10 tana rufe, Gwamna ya bude wata babbar kasuwar dabbobi a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin yin adalci ga kowane bangare a jihar.

Uba Sani ya ce zai ba manoma da makiyaya da kuma yan kasuwa dama domin cigaba da harkokinsu cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya bayyana yadda gwamnatin jihar ta hada kai da Gwamnatin Tarayya suka samar da kungiyar zaman lafiya da su ke aiki ba dare ba rana wurin ganawa da masu ruwa da tsaki, cewar TheCable.

Kaduna: Yadda aka samu mafitar ayyukan ta'addanci

"Mun yi ganawa da dama wanda ya kawo mana zaman lafiya, manyan yan bindiga sun ajiye makamansu da mabiyansu da dama."
"Jami'an tsaro sun yi namijin kokari wurin hallaka wasu yan bindiga da kuma taimakawa wurin kawo zaman lafiya."

- Uba Sani

Gwamna Uba Sani ya fara biyan sabon albashi

Kun ji cewa Gwamnatin Uba Sani ta fara aiwatar da sabon mafi karancin albashin N72,000 da ta yi wa ma'aikatan Kaduna alkawari a Oktoba.

Kara karanta wannan

Abba ya roki Sanusi II da sauran sarakunan Kano alfarma a kan tsare tsarensa

Sanarwa daga babban mataimaki ga Gwamna Uba Sani kan sababbin kafofin sadarwa, ta ce an fara biyan kudin daga watan Nuwambar 2024.

Gwamnatin jihar ta bukaci ma'aikatan Kaduna da su hanzarta kai koke ofishin babban akawun jihar idan sun ga gibi a albashin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.