'Yan Sanda Sun Dakile Harin 'Yan Ta'adda a Wani Musayar Wuta

'Yan Sanda Sun Dakile Harin 'Yan Ta'adda a Wani Musayar Wuta

  • Jami'an rundunar ƴan sanda na reshen jihar Imo sun samu nasara a yaƙin da suke yi da ƴan ta'adda masu tayar da ƙayar baya
  • Ƴan sanda sun daƙile wani harin ƴan ta'adda da ake zargin na ƙungiyar IPOB/ESN ne a ranar Talata, 29 ga watan Oktoban 2024
  • Jami'an tsaron sun sheƙe ɗaya daga cikin ƴan ta'addan tare da ƙwato makamai da mota a hannunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Imo - Rundunar ƴan sandan jihar Imo ta sanar da samun nasarar ɗakile wani harin ƴan ta'adda a ranar Talata.

Rundunar ƴan sandan ta ce ta samu nasarar hallaka ɗaya daga cikin ƴan ta'addan waɗanda ake zargin na ƙungiyar IPOB/ESN ne.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kori mutanen kauyuka 23 a kusa da sansanin sojoji

'Yan sanda sun dakile harin 'yan ta'adda a Imo
'Yan sanda sun kashe dan ta'adda a Imo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Henry Okoye, ya bayyana hakan ga manema labarai a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun daƙile harin ƴan ta'adda

Kakakin ƴan sandan ya kuma baje kolin gawar wanda ake zargin da kuma kayayyakin da aka ƙwato a hannun ƴan ta'addan a hedikwatar rundunar da ke Owerri, babban birnin jihar Imo.

Henry Okoye ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun kai harin ne lokacin da jami'an ƴan sanda ke aikin sintiri, rahoton The Punch ya tabbatar.

"A ranar 29 ga watan Oktoba, 2024, da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, tawagar yaƙi da ta’addanci ta yi nasarar daƙile wani hari da ake zargin ƴan ta’addan IPOB/ESN ne suka kai musu a lokacin da suke sintiri a kan titin Owerri/Aba."
"Kimanin mahara 10 ne suka ƙaddamar da harin wanda aka daƙile a motoci biyu. A yayin arangamar, an kashe mutum ɗaya, yayin da wasu suka gudu da raunuka, suka bar motarsu ƙirar Mercedes mai lambar Legas AAA 101 GR."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: 'Yan sanda sun cafke kansila kan yunkurin garkuwa da mutane

"Ƴan sandan sun ƙwato bindiga kirar AK-47, harsasai guda 15 masu 9.62mm, tutar ƙungiyar IPOB/ESN, da kuma motar da suka gudu suka bari."

- Henry Okoye

Ƴan sanda sun cafke ɗan majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja ta tabbatar da cafke dan majalisar wakilai, Hon. Alexander Mascot Ikwechegh.

Rahotanni sun ce ƴan sanda sun kama dan majalisar ne biyo bayan dukan da ya yi wa wani mai tuka motar haya a babban birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng