Yan Sanda Sun Fadi abin da Ya Jawo Gini Ya Rufta kan Mutane Masu Yawa a Abuja

Yan Sanda Sun Fadi abin da Ya Jawo Gini Ya Rufta kan Mutane Masu Yawa a Abuja

  • Rundunar 'yan sandan birnin tarayya Abuja sun yi karin haske game da wani gini da ya rufta kan mutane masu yawa
  • Ya zuwa yanzu an ceto mutane biyar yayin da rundunar ta ce ana kan gudanar da aikin ceton, inda ta aika sako ga jama'a
  • A zantawarmu da masani kan harkar gine-gine, Arch. Abdullahi Rabiu a Abuja, ya bayyana abubuwan da ke jawo gini rugujewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja ta tabbatar da rugujewar wani gini da ke a rukunin gidajen Vidaz a ranar Asabar.

Rukunin gidajen Vidaz ya na nan a Sabon Lugbe, cikin babban birnin tarayya Abuja kuma an ce ginin ya rufta ne kan mutane da dama.

Kara karanta wannan

'Abin takaici ne': Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan kiran juyin mulki, ta yi gargadi

Rundunar 'yan sanda ta yi magana bayan gini ya ruguje a Abuja
Yan sanda sun bayyana halin da ake ciki yayin da gini ya rufta kan mutane a Abuja. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Abin da ya jawo ginin Abuja ya ruguje

Rundunar 'yan sandan ta tabbatar da rugujewar ginin ne tare da bayyana halin da ake ciki a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken farko da rundunar ta yi ya nuna cewa a baya hukumomin babban birnin tarayya sun rusa ginin saboda an yi shi a wurin da aka mallaka ba bisa ka'ida ba.

Abin bakin ciki, masu satar karafa suka ci gaba da satar rodika da karafan ginin, lamarin da ya jawo ginin ya ruguje gabaki daya.

'Yan sanda sun bayyana halin da ake ciki

Wani bangare na sanarwar rundunar 'yan sandan ya ce:

"Binciken farko da muka gudanarwa ya nuna cewa a baya hukumomin babban birnin tarayya sun fcara rusa ginin saboda an yi shi a wurin da aka mallaka ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mutane 8 sun mutu a hatsarin jirgin sama, Tinubu ya sa ayi bincike

"Bayan haka ne masu satar karafa suka ci gaba da yin awon gaba da karafan ginin wanda ta kai ga ya ruguje gaba daya.
"An yi nasarar ceto mutane biyar daga cikin baraguzan ginin, kuma ba a samu asarar rai ba."

Rundunar ta bukaci jama'a da su mutunta iyakokin gine-gine da wuraren gine-gine da aka rusa, tare da tabbatar da tsaronsu da kuma hana afkuwar irin haka nan gaba.

Me ke jawo yawan ruftawar gine-gine?

A zantawarmu da masani kan harkar gine-gine, Arch. Abdullahi Rabiu a Abuja, ya ce ana samun yawaitar rushewar gine-gine saboda wasu dalilai da dama.

Arch. Abdullahi ya ce ana iya samun kuskuren farko daga wanda ya zana gidan, yana mai cewa kura-kurai a wajen kayyade adadin nauyin da gini zai iya dauka na jawo ruftawarsa.

Mai zane-zanen gidan ya ce idan ba a samu matsala daga zane ba, to ana iya samun matsala daga wadanda za su yi ginin, walau kin bin tsarin zanen, ko amfani da kayan aiki marasa kyau.

Kara karanta wannan

'Yadda 'yan ta'adda ke samun bindigogi da harsasan gwamnati,' sojoji sun yi bayani

Ya yi nuni da cewa kin kiyaye tsarin amfani da siminti, ruwa, yashi, duwatsu ko kuma kin yin amfani da kayan aiki masu kyau na sa gini ya rufta tun kafin ma a kammala shi.

Gini ya rufta kan jama'a a Abuja

Tun da fari, mun ruwaito cewa an shiga tashin hankali a Abuja bayan ruftawar wani gini a ranar Asabar a unguwar Sabon Lugbe da ke babban birnin.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa aƙalla mutane 40 ne suka maƙale a ginin, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar yayin da aka fara aikin ceto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.