ASUU Ta Zargi Gwamnati da Gaza Biyan Bukatunta, Ana Daura Damarar Yajin Aiki
- Kungiyar ASUU ta jaddada barazanar tafiya yajin aiki matukar gwamnati ta ki amincewa da biya mata bukatunta
- Shugaban kungiyar reshen jami'ar Nsukka, Raphael Amokaha ya jaddada matsayarsu yayin da gwamnati ke jan kafa
- Sai dai gwamnatin tarayya ta ma'aikatar ilimi ta ce an kafa kwamitin da zai yi aiki tukuru domin hana tafiya yajin aikin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Benue - Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa ta bayyana damuwa kan yadda gwamnatin tarayya ta ki magance bukatun da su ka mika mata.
Shugaban ASUU na reshen jami'ar Nsukka, Raphael Amokaha ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Makurdi.
Ƙungiyar ASUU na shirin tafiya yajin aiki
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kungiyar ta dakatar da yajin aikin da ta tsunduma a shekarar 2022 saboda nuna kishin kasa da ba gwamnati dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma a yanzu, gwamnati ta kara wasarere da matsalolin jami'o'in kasar nan, saboda haka akwai shirin tafiya yajin aiki matukar ta ci gaba da nuna halin ko-in-kula.
ASUU ta dora alhakin yajin aiki kan gwamnati
Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa ta ce tun a shekarar 2022 ta ke kokarin ganin gwamnati ta yi abin da ya dace wajen inganta ilimin jami'o'i da malamansu.
Ya gargadi gwamnati da ta dauke su da muhimmanci, domin akwai shirin tafiya yajin aikin gama gari idan aka ci gaba da barin ilimin jami'o'i cikin mawuyacin hali.
Gwamnati ta dauki barazanar ASUU da gaske
A baya mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta fara daukar batun barazanar yajin aikin da gaske domin yanzu haka ma'aikatar ilimi ta fara daukar matakin hana su tafiya yajin aiki.
Daraktan yada labarai na ma'aikatar ilimi ta kasa, Folasade Biriowo, ya bayyana cewa ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya samar da wata tawaga da za ta yi aiki da ASUU domin hana yajin aikin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng