Yadda Matasa Suka Tsere daga Kurkukun Bello Turji bayan Ya Saka Ranar Harbe Su

Yadda Matasa Suka Tsere daga Kurkukun Bello Turji bayan Ya Saka Ranar Harbe Su

  • Wasu matasan garin Moriki a jihar Zamfara sun kubuta daga hannun babban dan ta'adda, Bello Turji bayan ya yi musu barazanar kisa
  • Turji ya yi holon matasan a wani bidiyo yana cewa idan ba a kawo masa kudin fansa ba zai kashe su kamar yadda aka yi wa Sarkin Gobir
  • Sai dai duk da haka akwai wasu mata guda shida a hannun dan ta'addar daga garin Moriki duk da cewa bai yi musu barazanar kisa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Wasu matasa sun kubuta daga hannun dan ta'adda, Bello Turji bayan ya yi alkawarin kashe su.

Ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji ya kama matasan ne daga garin Moriki inda ya ce ko a hada masa kudin fansa ko ya kashe su.

Kara karanta wannan

'Bello Turji na kokarin sauya suna': Bulama ya fallasa shirin hatsabibin dan bindiga

Matasan Moriki
Matasan Moriki sun kubuta a hannun Bello Turji. Hoto: Bala Danjuma
Asali: Facebook

Lauya mai fashin baki, Audu Bulama Bukarti ne ya wallafa cewa matasan sun kubuta a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bello Turji ya yi alkawarin kashe matasa

Bello Turji ya sake wani bidiyo inda yake cewa zai kashe matasan a yau Alhamis matuƙar ba a kawo masa kudi ba.

Dan ta'addar ya ce zai kashe su ne a yau Alhamis da karfe 02:00 na rana idan mutanen Moriki ba su hada masa N30m ba.

Yadda matasan suka tsere daga hannun Turji

Bayan matasan sun tabbatar dan ta'addar zai kashe su, sai suka yanke shawarar su gudu cikin dare.

Bayan sun gudu, matasan sun samu kubuta kuma uku daga cikinsu sun isa garin Moriki yayin da ake jiran isowar biyu daga cikinsu.

Saura mata 6 a hannun Bello Turji

Sai dai duk da cewa mazan sun kubuta, har yanzu akwai wasu mata shida a hannun Bello Turji daga garin Moriki.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: An tono gawar matashin da aka birne a daƙi, an kama mutum 1

Duk da cewa a karon farko bai yi alkawarin zai kashe su ba, ba a san me dan ta'addar zai fada a kansu ba a halin yanzu.

An kama harsashi a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa asirin wani mai sayen makami da kayan fada ga yan bindiga masu garkuwa da mutane ya tonu a jihar Katsina.

Yan sa kai a jihar Katsina sun kama tulin harsashi yayin da mutumin ya ɓoye su a cikin wata motar haya da ke tafiya zuwa garin Batsari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng