Manyan Abubuwa da aka Wayi Gari da Su a Maiduguri bayan Ambaliya

Manyan Abubuwa da aka Wayi Gari da Su a Maiduguri bayan Ambaliya

  • Hankula sun fara kwanciya bayan an yi fama da mummunar ambaliyar ruwa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno
  • Al'umma sun fara komawa gidajensu domin duba halin da suke ciki da yadda za su yi gyare-gyare domin komawa cikinsu
  • An bayyana yadda mutane da dama suka kwana a bakin hanya saboda rashin wajen da za su kwanta da ambaliyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Rahotanni sun bayyana yadda aka wayi gari a Maiduguri bayan an kwana da ambaliyar ruwa.

An hango mutane dauke da kayayyakinsu suna tafiya a kan tituna yayin da ambaliyar ta fara lafawa sosai.

Ambaliyar ruwa
Ambaliya ta fara sauki a Maiduguri. Hoto: Bulama Adamu
Asali: Getty Images

Legit ta tatttaro yadda aka wayi gari a Maiduguri ne a cikin wani bidiyo da Muhammad A. Umar ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Mutane sama da 200,000 sun rasa gidaje, yara sun bace a Maiduguri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ambaliya ta fara lafawa a Maiduguri

Cikin manyan abubuwan da aka wayi gari da su na farin ciki akwai ganin ambaliyar ta lafa sosai a safiyar yau Laraba.

An hango mutane da dama suna tafiya a kan tituna, wasu da kafa wasu da abubuwan hawa ta wuraren da babu halin wucewa a yammacin jiya.

Mutane sun kwana a bakin hanya

Da safiyar yau an hango tulin kaya a bakin hanyoyin Maiduguri inda wasu mutane suka kwana bayan ruwa ya cika gidajensu.

Kusan duk inda mutum ya wuce zai ga mutane a zaune a bakin hanya tare da 'yan kayansu suna bukatar taimako.

An ruwaito cewa mutane da dama sun kwana ne a karkashin bishiyoyi kasancewar wuraren kwana sun yi kadan.

Mutane sun fara komawa gidajensu

Sakamakon fara raguwar ambaliyar, wasu mutane sun fara komawa gidajensu domin duba halin da suke ciki.

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu: Malami ya hango shekarar da tsadar rayuwa za ta kare a Najeriya

Sai dai har yanzu wasu ba su iya shiga gidajensu kasancewar ambaliyar ba ta gama tsayawa sosai a wasu wuraren ba.

Haka zalika masu ba da agajin gaggawa na cigaba da ba al'umma tallafin abinci a wurare da dama na Maiduguri.

An rasa gidaje da dama a Maiduguri

A wani rahoton, kun ji cewa bayanai sun fara fitowa kan irin asarar da aka tafka a Maiduguri sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye garin.

Rahotanni da suka fito na nuni da cewa mutane sama da 200,000 ne suka rasa gidajen zamansu a dalilin mummunar ambaliyar ruwan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng