An Shiga Jimami, 'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane, Sun Sace Wasu da Dama a Arewa

An Shiga Jimami, 'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane, Sun Sace Wasu da Dama a Arewa

  • Wasu miyagun ƴan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna
  • Ƴan bindigan sun hallaka mutum biyar tare da sace wasu da dama a harin da suka kai a ƙauyen Kallah Afogo a garin
  • Miyagun sun kuma kai wani hari a ƙauyen Bakin Pah inda suka yi garkuwa da wasu mutum shida zuwa cikin daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƴan bindiga sun kashe mutane biyar tare da yin garkuwa da wasu da dama a jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Kallah Afogo a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Kaduna
'Yan bindiga sun kai hare-hare a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke mata masu ba 'yan bindiga bayanai a jihar Kaduna

Jaridar Daily Trust ta ce mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan bindigan sun kai farmaki a ƙauyen ne da misalin ƙarfe 11:15 na daren ranar Lahadi.

Waɗanda aka kashe a ƙauyen Kallah sun haɗa da Garkuwa Alfarma, Buhari Maidiga, Uba Auta, Yakubu Thomas Gaku, da Atabata Naallah.

Ɗaya daga cikin waɗanda ƴan bindigan suka kashe, sun hallaka shi ne bayan ya bi su zuwa cikin daji sannan suka yanke masa kai.

Hakazalika, ƴan bindigan sun sake kai wani hari a ƙauyen Bakin Pah da ƙaramar hukumar, inda suka kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da wasu mutum shida.

Wani ɗan yankin mai suna Maigari Ben ya yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara tsaurara tsaro a yankin tare da tabbatar da cewa an kuɓutar da mutanen da aka sace.

Kara karanta wannan

Babban alkali ya kubuta daga hannun 'yan ta'adda bayan kwashe watanni a tsare

Me ƴan sanda suka ce kan harin?

Legit Hausa ta yi ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Sai dai, bai dauki kiran wayar da aka yi masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Sojoji sun cafke masu ba ƴan bindiga bayanai

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun kama wasu mata guda biyu da ake zargin masu ba ƴan bindiga bayanai ne a Kaduna.

Sojojin sun cafke matan ne da ake zargin suna haɗa baki da ƴan bindiga a ƙauyen SCC da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng