"Uwa ce ga Kowa," Dan Majalisa Ya Yi Jimamin Rasuwar Mahaifiyar Shugaba 'Yar'Adua

"Uwa ce ga Kowa," Dan Majalisa Ya Yi Jimamin Rasuwar Mahaifiyar Shugaba 'Yar'Adua

  • Dan majalisar wakilai, Abdullahi Aliyu Ahmad ya mika ta'aziyyar rasuwar uwar tsohohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar'adua
  • Hajiya Dada Musa 'Yar'adua ta rasu a ranar Litinin bayan ta shafe shekaru 102 a bayan kasa, 'dan majalisa ya aika da ta'aziyyarsa
  • Ho. Abdullahi Aliyu Ahmad ya taya al'umar Katsina da iyalan marigayiyar jimamin rashinta, ya yi addu'ar Allah ya gafarta mata

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Yayin da dubban musulmi suka rika tururuwa zuwa gidan 'Yar'adua, shugaban kwamitin harkokin cikin gida, Hon. Abdullahi Aliyu Ahmad ya shiga jerin masu ta'aziyya.

Hajiya Dada Musa 'Yar'adua, mahaifiyar tsohon shugaban kasar nan, marigayi Umaru Musa 'Yar'adua ce ta kwanta dama a ranar Litinin ta na da shekaru 102 a duniya.

Kara karanta wannan

"Haduwata ta karshe da ita": Saraki ya yi alhinin mutuwar mahaifiyar Yar'adua

Katsina
Dan majalisa ya yi ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar tsohon shugaban kasa 'Yar'adua Hoto: Adewale Kareem/Hon. Abdullahi Aliyu Ahmad
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa dan majalisar ya taya gwamnatin jihar Katsina da al'umar jihar baki daya alhinin rashin dattijuwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan majalisa ya yi ta'aziyyar Dada Yar'adua

A sanarwar da, Sardauna Francis, mataimaki na musamman kan yada labaran dan majalisar ya fitar, an yi addu'ar Allah ya gafartawa mahaifiyar tsohon shugaban kasar.

Dan majalisar ya bayyana marigayiya Hajiya Dada Musa Yar'adua a matsayin mace mai kamar maza, wacce ta raini jajirtattun mazaje da suka jagoranci kasar nan.

Dan majalisar da ke wakiltar Musawa/Matazu a jihar Katsina ya bayyana marigayiwar da uwa ga kowa, da ba ta nuna banbancin yare, addini ko siyasa, inda ya kara addu'ar Allah ya mata rahama.

Dada Yar'adua: Shugaba Tinubu ya yi ta'aziyya

A wani labarin mun ruwaito cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana kaduwa bisa rasuwar mahaifiyar tsohon shugaban kasa, marigayi Umaru Musa 'Yar'adua.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kadu da rasuwar mahaifiyar Yar'Adua, ya fadi alherin da ta shuka

Hajiya Dada Musa 'Yar'adua ta rasu a ranar Litinin a babban asibitin tarayya da ke jihar Katsina ta na da shekaru 102 a duniya, kuma tuni an yi mata sutura kamar yadda addini ya tanada.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.