Dattawan Delta Sun Raba Gari da Tinubu kan Kalamansa, Siyasarsa ta Samu Koma Baya

Dattawan Delta Sun Raba Gari da Tinubu kan Kalamansa, Siyasarsa ta Samu Koma Baya

  • Kungiyar Obedient Elders' Council ta yi zazzafan martani ga Bola Ahmed Tinubu kan maganar da ya yi a kan masu zanga zangar tsadar rayuwa
  • Kungiyar ta ce maganar da shugaban kasa ya yi tana nuna cewa tamkar bai san halin kuncin da talakawa ke ciki a Najeriya ba ne
  • Haka zalika kungiyar ta yi magana kan rikici da sace sace da aka samu a wasu jihohi a lokacin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - Kungiyar Delta Obedient Elders' Council ta yi martani mai zafi ga gwamnatin tarayya kan zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Bayan zanga zanga, mai neman takaran shugaban kasa a APC ya caccaki gwamnati

Kungiyar ta ce an saka rai wajen samun sauki amma sai Bola Tinubu ya yi maganar da ba ta dauki hanyar kawo sauki ba.

Bola Tinubu
Kungiya ta soki Tinubu kan zanga zanga. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugaban kungiyar, Chris Biose da sauran yan kungiyar ne suka sanya hannu kan sakon da suka wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meye Tinubu bai fada a jawabinsa ba?

Kungiyar Obedient Elders' Council ta ce akwai bukatar shugaban kasa ya yi magana a kan abubuwan masu muhimmanci kamar kisan mutane da ake zargin yan sanda sun yi.

Ta ce bai yi magana a kan yadda ake kashe manona ba da yadda zai magance matsalar duk da cewa hakan ne ke yawan jawo yunwa a Najeriya.

Biose: 'An saka tsammani kan Tinubu'

Shugaban kungiyar, Chris Biose ya ce mutane da dama sun saka ran jin maganganu da za su kwantar musu da hankali yayin jawabin shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: A karshe, Ganduje ya yi magana, ya tura sako ga 'yan Najeriya

Sai dai ya ce abin takaici ne yadda maganganunsa suka zama kamar bai ma san me yake faruwa a fadin Najeriya ba.

Maganar tayar da hankula a jihohi

Haka zalika kungiyar ta yi martani kan yadda aka samu tashin hankula da kashe kashe a wasu jihohi a lokacin zanga zangar.

Obedient Elders' Council ta ce abin Allah wadai ne yadda hakan ta faru kasancewar ana fama da matsanancin halin rayuwa.

Zanga zanga: An kai hari gidan Sanata

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Ibrahim Bomai ya yi martani bayan wasu da ake zargi suna cikin masu zanga zangar tsadar rayuwa sun kai hari gidansa.

Sanata Ibrahim Bomai mai wakiltar Yobe ta Kudu ya zargi yan siyasa a ciki da wajen jami'yyar APC da zuga matasan wajen kai hari gidansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng