Sarautar Kano: Abin da Sarki Sanusi II Ya Gargadi Hakimai da Ciyamomi 44 a Kai a Fadarsa

Sarautar Kano: Abin da Sarki Sanusi II Ya Gargadi Hakimai da Ciyamomi 44 a Kai a Fadarsa

  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya ja hankalin iyayen yara kan kula da tarbiyar 'ya'yansu domin samar da al’umma mai inganci
  • Sarkin ya bayyana haka ne yayin da hakimai da shugabannin riko na kananana hukumomi 44 suka kai masa ziyara
  • Mai Martaba ya shawarci iyaye da su tabbatar da kula da duka shige da ficen 'ya'yansu wurin kare su daga shiga harkar kwaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gargadi iyayaen yara wurin tarbiyantar da 'ya'yansu kan tafarki mai kyau.

Sarkin ya ce iyaye suna da muhimmiyar rawa da za su taka wurin tabbatar da tarbiyar 'ya'yansu a cikin al’umma.

Kara karanta wannan

Kano: Hakimai da shugabannin kananan hukumomi 44 sun ziyarci Sanusi II, fada ta cika maƙil

Sarki Sanusi II ya ja hankalin iyayen yara kan tarbiya a Kano
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bukaci iyaye su kula da tarbiyar 'ya'yansu. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi.
Asali: Facebook

Jan hankali da Sanusi II ya yi

Sanusi II ya ja kunnensu da su saka ido kan 'ya'yansu domin tabbatar da kare su daga miyagun kwayoyi da kuma halaye marasa kyau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon sarkin ya bayyana haka ne ta bakin Wazirin Kano, Sa’adu Gidado a fadarsa a jiya Asabar 1 ga watan Yuni, cewar The Nation.

Hakan ya biyo bayan caffan ban girma da hakimai da shugabanin kananan hukumomi 44 da limaman yankin Kano ta Tsakiya guda 15 suka kai masa.

”Ku yi ta addu’a ba kakkautawa domin samun zaman lafiya da ci gaban al’umma a jihar Kano dama kasa baki daya.”

- Muhammadu Sanusi II

Musabbabin ziyarar ciyamomi fadar Sanusi II

Shugaban riko na karamar hukumar Tarauni, Abdullahi Maikano ya ce sun kai ziyara fadar sarkin domin yin mubaya’a gare shi.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rikicin sarautar Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi nadin farko

Maikano ya ce samun Sanusi II a matsayin Sarki babbar kyauta ce daga Allah wanda zai amfani jihar gaba daya ta bangarori da dama.

Hakimai sun kai ziyara fadar Sanusi II

A wani labarin, kun ji cewa hakimai da dama da dagatai daga kauyuka sun kai ziyara fadar Sarki Muhammadu Sanusi II a Kano.

Hakiman sun kai ziyarar da shugabannin riko na kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar domin yin mubaya’a ga sarkin.

Wannan na zuwa ne bayan mayar da sarkin kan kujerarsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a ranar 23 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.