Rundunar Sojoji Ta Ayyana Neman Halilu Buzu Ruwa a Jallo Bisa Zargin Ta'addanci a Zamfara

Rundunar Sojoji Ta Ayyana Neman Halilu Buzu Ruwa a Jallo Bisa Zargin Ta'addanci a Zamfara

  • Sojojin Najeriya sun bayyana Halilu Buzu a matsayin wanda suke nema ruwa a jallo bisa zargin aikata miyagun laifukan ta'addanci
  • Bayanai sun nuna cewa Halilu, wanda ya tara yara a dajin Zamfara ya tsallake zuwa jamhuriyar Nijar domin neman mafaka
  • Rundunar sojin ta ce tuni ta fara aiki da sojojin Nijar da nufin kamo ɗan ta'addan, wanda ya shahara wajen aikata manyan laifuka a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rundunar sojoji ta bayyana Halilu Buzu a matsayin wanda take nema nema ruwa a jallo bisa ayyukan ta’addanci, safarar makamai, haƙar ma'adanai ba bisa ka’ida ba da satar shanu.

Mai magana da yawun hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), Manjo Janar Edward Buba ne ya sanar da haka a wurin taron manema labarai na mako-mako a Abuja.

Kara karanta wannan

Tsohon Sanata a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 98

Manjo Janar Edward Buba.
Sojoji na neman Halilu Buzu ruwa a jallo bayan ya gudu ya bar ƙasar Hoto: Defence HQ Nigeria
Asali: Facebook

Sojoji na neman Halilu Buzu

Ya bayyana cewa Halilu Buzu ɗan asalin Neja, wanda ya tare a dajin jihar Zamfara ya tsallake zuwa Jamhuriyar Nijar domin neman mafaka, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojan ya ce wanda ake zargin ya tsere zuwa Jamhuriyar Nijar bayan kaddamar da hare-haren ta'addanci a Najeriya, kuma yana da yara a ƙarƙashinsa da yawa.

Janar Buba ya ce tuni rundunar sojoji ta fara aiki tare da takwarorinta na Jamhuriyar Nijar, domin tabbatar da cafke dan ta'addan.

Nasarorin sojoji a mako 2 a Najeriya

A rahoton The Cable, Buba ya kuma ce dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar ceto jimillar mutane 253 da aka yi garkuwa da su a cikin makonni biyu da suka gabata.

A cewarsa, sojojin rundunar Operation Y-Watch, da dakarun rundunar sintirin yaki, da dakarun rundunar Operation Delta ne suka cimma wannan nasarorin.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun kama rijiyoyin mai na bogi a jihar Ribas

Kakakin hedikwatar tsaron ya ci gaba da cewa dakarun sojojin sun murƙushe ƴan ta'adda 227 tare da cafke wasu 529, sun kuma kama ɓarayim mai 11 a cikin mako biyu.

"Muna ci gaba da kai hare-hare kan wadannan nau'ukan ƴan ta'adda ta yadda za mu kawar da su gaba ɗaya, mu kakkaɓe su daga fagen fama cikin ƙanƙanin lokaci," in ji shi.

Amnesty ta tsoma baki kan kisa matashi

A wani labarin kuma ana zargin jami'an ƴan sanda sun yi sanadin mutuwar wani matashi, Kabiru Ibrahim a kauyen Soro a jihar Bauchi.

Kungiyar kare haƙkin ɗan adam, Amnesty, ta bayyana cewa ƴan sanda sun aikata wannan mummunan laifin ne kan wanda ake zargi da sata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel