An Yi Garkuwa da Mutane 5 a Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Kai Hari Abuja

An Yi Garkuwa da Mutane 5 a Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Kai Hari Abuja

  • Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne a daren ranar Asabar din da ta gabata sun kai hari a garin Dutse Makaranta da ke a Abuja
  • Daga bayanan da aka samu, 'yan bindigar sun mamaye Dutse ta yankin garin Mpape inda suka yi awon gaba da mutane biyar
  • Wannan harin dai ya jefa al’ummar Dutse cikin fargaba tare da nuna damuwa game da karuwar rashin tsaro da ya addabi yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bwari, Abuja - ‘Yan bindiga sun kai farmaki garin Dutse da ke wajen babban birnin tarayya Abuja a daren ranar Asabar, inda suka yi awon gaba da akalla mutane biyar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe mutane 3 a Zamfara, fusatattun matasa sun yi zanga-zanga

"Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 5 a wani hari da suka kai Abuja
An ruwaito 'yan bindigar sun lakadawa wata mahaifiya dukan tsiya, suka kuma tafi da yaranta. Hoto: @Jossy_Dannyking
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun mamaye kauyen Abuja

‘Yan bindigar sun mamaye garin ne ta wani yanki mai tudu da ke hade da yankin da Mpape, wani gari da ke a cikin Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Nation ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun isa garin Duste mai yalwar bishiyar da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar.

Wani mazaunin yankin da ba ya so a buga sunansa ya ce wadanda ke zaune a yankin ba su iya yin barci a daren ba har gari ya waye sakamakon fargaba.

"Sun lakadawa wata uwa duka" - Majiya

Majiyar ta ce:

"Sun zo da misalin karfe 8 na dare inda suka yi garkuwa da mace daya, magidanta uku da yara biyu. Amma a safiyar Lahadi mun tsinci daya daga cikin yaran da aka sace a cikin daji."
"'Yan bindigar sun lakadawa mahaifiyar yaran biyu da ke cikin wadanda suka sace dukan tsiya, yanzu haka tana kwance a asibiti."

Kara karanta wannan

Neja: An shiga fargaba bayan 'yan bindiga sun sake hallaka sojoji tare da sace Kyaftin

Mazauna Dutse sun shiga faragaba

Harin dai ya jefa al’ummar Dutse cikin fargaba tare da nuna damuwa game da karuwar rashin tsaro da ya addabi yankin, jaridar Leadership ta ruwaito.

Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da an dawo da mutanen da aka sace.

Ya zuwa yanzu dai ba a ji ta bakin jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh a kan lamarin ba.

An kama malamin tsibbu a Osun

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa rundunar 'yan sanda a jihar Osun ta kama wani malamin tsibbu da abokansa bisa zargin sun kashe wata bafullatana.

Malamin tsibbun wanda ya amsa laifinsa ya bayyana cewa shi da abokansa sun kona wasu sassa na matar tare da hadawa da hanjin alade da akuya domin yin tsafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel