Wani Mutum ya Kona Masallata su na Tsakar Sallar Asubahi a Kano

Wani Mutum ya Kona Masallata su na Tsakar Sallar Asubahi a Kano

  • Wani mutum da har yanzu ba a kai ga gano ko waye ba ya cinnawa masallata wuta a Larabar Abasawa da ke karamar hukumar Gezawa a jihar Kano
  • Rahotanni sun ce akalla masallata kimanin 40 su ke sallar asubahi lokacin da mutumin ya zazzaga musu man fetur sannan ya cinna musu wuta
  • Yanzu haka an kai wasu mutane 20 daga cikinsu asibitin Murtala domin ba su agajin gaggawa, yayin da ake jiran samun karin bayani kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano-Wani mutum da ba a gane ko waye ba, ya kone wani masallaci a garin Larabar Abasawa da ke yankin karamar hukumar Gezawa a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Operation kauda badala: Hisbah ta damke maza da mata 20 suna wanka tare a Kano

Rahotanni sun ce, wannan al’amari da ya faru da asubahin Larabar nan, ya yi sanadin konewar masallata da dama, bayan da mutumin ya yi amfani da fetur inda ya kunnawa masallacin wuta, lokacin da akalla mutane arba’in ke sallar asubah.

Kano yan sanda
An kama mutumin da ya cinnawa masallata wuta Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa an gaggauta kai ashirin daga cikin wadanda suka samu mummunar kuna zuwa asibitin Murtala da ke nan cikin birni, domin samun agajin farko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waye ya kona masallacin?

Shafi'u Abubakar, mai shekaru 38 da haihuwa ne mutumin da rundunar 'yan sandan Kano ta kama bisa zargin kunna wuta a masallacin Gezawa.

Tuni dai ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, domin a garin jefa wutar ne ma ya kone a hannuwansa guda biyu, kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya wallafa a shafinsa na facebook.

Kara karanta wannan

"Daurarru 400 a Kano ba su san makomarsu a gidan yari ba," Inji 'Yan Sanda

Bincike sun gano cewa dambarwar gado ce ta sanya Shafi'u Abubakar kunna wannan wuta, ana ci gaba da zurfafa bincike, inji SP kiyawa.

'Yan sanda sun tabbatar da kone masallaci

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa da Legit Hausa ta tuntube shi ya tabbatar da harin, inda ya ce tuni su ka kama wanda ya kai harin yayin da ake ci gaba da bincike.

Ya ce zuwa yanzu mutum 24 aka samu nasarar kai wa asibitin Murtala inda su ke karbar magani da ci gaba da duba su.

An sace malami a Kogi

Mun ba ku labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari jihar Kogi inda su ka sace babban limamin Iyara dake karamar Ijumu, Sheikh Quasim Musa yayin da musulmi ke kokarin buda baki.

‘yan bindigar sun shiga garin suna harbin mai uwa da wabi, wanda ya jefa al’uma cikin rudani, kafin nan su sace malamin.

Kara karanta wannan

"Wannan ai sata ce," NLC ta magantu kan karin kudin wutar lantari a Kogi

Asali: Legit.ng

Online view pixel