Gwamna Abba Kabir Ya Yi Ƙus-Ƙus da Ministan Tinubu da Jigon APC a Kano, Bayanai Sun Fito

Gwamna Abba Kabir Ya Yi Ƙus-Ƙus da Ministan Tinubu da Jigon APC a Kano, Bayanai Sun Fito

  • Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma, Mohammed Idris, ya kai ziyara ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a ofishinsa na gidan gwamnatin Kano
  • Idris ya je Kano ne a wata ziyarar aiki ta tsawon kwanaki biyu, inda ya gana da masu kafafen watsa labarai, kwararru da ƴan kasuwa
  • Bashir Ahmad, tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, na cikin tawagar da suka ziyarci Abba a ofishinsa ranar Jumu'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi bakuncin ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris a gidan gwamnatin jihar Kano.

Mohammed Idris da Abba Kabir.
Minista ya ziyarci Abba Gida-Gida Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

Ministan ya kai ziyara ta musamman da Gwamna Abba Kabir ne a fadar gwamnati da ke birnin Kano da safiyar ranar Jumu'a, 22 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta bayyana: Jigon LP ya bayyana dalilin da yasa Peter Obi ya yi buda-baki da Musulmai

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ne ya bayyana haka a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene maƙasudin wannan ziyara?

Ya ce ministan yaɗa labarai ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu ne a Kano, inda ya gana da shugabannin kafafen watsa labarai, kwararru da ƴan kasuwar jihar.

A sanarwan da ya wallafa a shafinsa, Bashir Ahmad ya ce:

"Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya ziyarci mai girma gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a ofishinsa da ke gidan gwamnatin Kano.
Ministan ya kawo ziyarar aiki ta kwanaki biyu a nan Kano, kuma ya tattauna da shugabannin kafafen yada labarai da kwararru da kuma ‘yan kasuwar jihar Kano."

Tsohon hadimin Buharin na cikin tawagar da suka raka Idris zuwa gidan gwamnatin Kano domin ganawa da Abba Gida-Gida.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Malam Nasiru El-Rufa'i ya gana da fitaccen sanatan PDP, hotuna sun bayyana

Wannan na zuwa ne watanni bayan tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, ya roƙi Abba ya jefar da jam'iyyar NNPP, ya taho su haɗu a APC mai mulkin Najeriya.

Gwamna Uno na tare da Tinubu

A wani rahoton kuma duk da banbancin jam'iyyun siyasa, gwamnan jihar Akwa Ibom ya ce ba zai yarda ya taƙali faɗa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba.

Fasto Umo Eno ya gargaɗi mambobin PDP da ɗaruruwan masu sauya sheka zuwa jam'iyyar su guji zagin shugabanni kamar Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel