Gwamnatin Kano Ta Kaddamar da Shirin Ba da Tallafin N260m Ga Mata 5,200 Duk Wata

Gwamnatin Kano Ta Kaddamar da Shirin Ba da Tallafin N260m Ga Mata 5,200 Duk Wata

  • Akalla mata 5,200 daga kananan hukumomi 44 na jihar Kano ne za su rika karbar tallafin Naira 50,000 kowacce a duk wata
  • Gwamna Abba Yusuf na jihar ya bayyana hakan a ranar Laraba, 15 ga Mayu, inda ya ce shirin zai gudana har karshen mulkinsa
  • Gwamnan ya jaddada cewa, shirin wanda zai rika lakume Naira miliyan 260 duk wata an bullo da shi domin nuna godiya ga matan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shirinta na ba kananu da matsakaitan 'yan kasuwa mata tallafin N50,000 kowacce a duk wata.

Gwamnatin ta ce za a rika zakulo mata 5,200 a kowanne wata domin ba su wannan tallafin.

Kara karanta wannan

"An yi amfani da bam": Mutum 1 ya mutu da aka bankawa masallata wuta a Kano

Abba Yusuf ya bullo da shirin tallafawa matan Kano
Gwamnatin Abba Yusuf a Kano za ta fara ba mata tallafin N50,000 kowane wata. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Facebook

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf wanda ya bayyana hakan a shfinsa na Twitter a ranar 15 ga watan Mayu, ya kuma ce matan za su fito ne daga kananan hukumomi 44 na jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za a tallafawa mata da N260m" - Gwamnan Kano

A cewar Abba Yusuf, gwamnatin jihar za ta rika kashe Naira miliyan 260 a kowane wata domin ba da tallafin har wa'adin mulkinsa ya kare.

Mai girma gwamnan ya ce:

"Hukumar sake daidaita rayuwar al'umma (CRC) ce za ta rika gudanar da rabon, wanda za a zabo mata dari-dari daga kowace karamar hukuma a cikin kananun hukumomi 36 na wajen birnin Kano.
"Za kuma a tallafawa a mata dari biyu-biyu daga kowace karamar hukuma a cikin kananun hukumomi 8 na cikin birnin Kano."

Gwamnan jihar ta Kano ya jaddada cewa wannan shirin an yi shi ne domin nuna godiyar su ga mata saboda gagarumar gudunmawar da suka bayar a zaben shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: EFCC ta na neman gwamnan PDP ruwa a jallo? Gaskiya ta fito

"Tinubu ya yi watsi da mu" - Matan APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar shugabannin matan APC sun koka kan yadda suka ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da su bayan zaben 2023.

Matan sun yi magana kan kin ba su mukami ko daya a gwamnati da kuma nuna masu wariya da ake yi idan aka zo rabon tallafin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.