Gwamnatin Tinubu Na Tunanin Kwashe Kuɗin Ƴan Fansho Ta Yi Wasu Muhimman Ayyuka

Gwamnatin Tinubu Na Tunanin Kwashe Kuɗin Ƴan Fansho Ta Yi Wasu Muhimman Ayyuka

  • Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta fara shirin kashe kuɗin ƴan fansho domin gudanar da wasu ayyuka
  • Ministan kuɗi, Wale Edun ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala taron FEC na kwanaki biyu a fadar shugaban ƙasa ranar Talata
  • Ya ce gwamnati na shirin gina gidaje da kuma bayar da su haya na tsawon lokaci domin inganta rayuwar ƴan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da shirinta na ɗaukar kudade kamar kuɗin fansho da kudin inshorar lafiya don zuba ayyukan more rayuwa a kasar nan.

Ministan Kudi da tattalin arziki na ƙasa Wale Edun ne ya bayyana hakan a jiya Talata yayin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnati da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Badaƙalar N19.4bn: An samu matsala yayin gurfunar da Ministan Buhari da ɗan uwansa a kotu

Tinubu da Wale Edun.
Gwamnatin tarayya ta fara tunanin amfani da kuɗin ƴan fansho Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Wale Edun
Asali: Twitter

Ya faɗi wannan shirin na gwamnatin ne bayan kammala taron kwanaki biyu na majalisar zartarwa (FEC) wanda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce akwai sama da N20trn na irin wadannan kudade a jigbe, inda ya ce za a zuba su wajen gina ababen more rayuwa kamar gidaje da jinginar da su na dogon lokaci.

Gwamnatin Tinubu za ta kashe kuɗin fansho

A ruwayar Leadership, Wale Edun ya ce:

"Najeriya ƙasa ce mai juriya, ’yan Najeriya suna da juriya kuma a zahirin gaskiya tun kafin mu fara neman masu zuba jari daga kasashen waje, mun fara neman yadda za a samu kuɗaɗe, mun gano muna da su a Najeriya.
"Kuɗin fansho, inshorar lafiya da kuɗin asusun zuba jari gaba ɗaya, kuɗin da za a jima ba a waiwaye su ba, zamu zuba su a ayyukan more rayuwa a faɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shiga muhimmin taro a Villa, ya rantsar da sababbin kwamishinoni 2

"Muna da sama da N20trn na irin waɗannan kuɗaɗen, kuma kamar kuɗin fansho abu ne da ba yanzu zai kare ba, mutane na aje kuɗin a tsawon rayuwarsu."

Ministan ya ƙara da cewa bayan tattaunawa da ɓangaren da ya dace, gwamnati na shirin zuba waɗannan kuɗaɗe domin samar da ababen more rayuwa kamar gina gidaje.

Jerin ma'aikatun da ake bi kuɗin wuta

A wani rahoton kuma ma'aikatun gwamnati sama da 34 ne ake bi bashin kudin wutar lantarki duk da cewa suna karbar kudin wuta duk shekara.

Cikin jerin manyan ma'aikatun da ake bi bashi sosai har da fadar shugaban kasa da hedikwatar sojin da 'yan sandan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel