Yahaya Bello: Kotu Ta Umarci Shugaban EFCC Ya Gurfana a Gabanta, Ta Jero Dalilai

Yahaya Bello: Kotu Ta Umarci Shugaban EFCC Ya Gurfana a Gabanta, Ta Jero Dalilai

  • Yayin da ake cece-kuce game da tuhumar da ke kan tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, kotu ta ba da sabon umarni
  • Babbar kotun jihar da ke zamanta a birnin Lokoja ta umarci shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya hallara a gabanta
  • Kotun ta dauki wannan mataki ne kan zargin shugaban hukumar da saba umarnin da ta bayar kan binciken Yahaya Bello

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Babbar kotun jihar Kogi ta ba da umarni ga shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya gurfana a gabanta.

Kotun ta umarci shugaban hukumar ya tabbatar ya amsa kira zuwa ranar 13 ga watan Mayun 2023 kan saɓa umarninta.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da dambarwar Yahaya Bello, Hukumar EFCC ta yi garambawul a mukamai

Kotu ta ba da sabon umarni kan shugaban EFCC game da binciken Yahaya Bello
Kotu a jihar Kogi ta umarci shugaban EFCC ya hallara a gabanta kan badakalar Yahaya Bello. Hoto: Yahaya Bello, @officialEFCC.
Asali: UGC

Wane zargi ake yi wa shugaban EFCC?

Shugaban hukumar na fuskantar tuhume-tuhume kan zargin ci gaba da ɗaukar wasu matakai bayan umarnin kotun, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin ba da umarnin, alkalin kotun, Mai Shari'a, I. A Jamil ya de hukumar ta saba dokar da aka gindaya mata wurin aiwatar da wasu ayyuka kan binciken Yahaya Bello.

Alkalin kotun ya yi hukuncin ne kan korafin da lauyan Yahaya Bello, M. S Yusuf ya shigar kan saɓa doka da hukumar ta yi, cewar TheCable.

Umarnin da kotun ta ba shugaban EFCC

Jamil ya umarci shugaban hukumar ya hallara a gabanta domin amsa tambayoyi kan zargin saɓa umarninta.

Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta yi wa gidan tsohon gwamnan ƙawanya kan zargin badakalar N84bn lokacin da ya ke mulki.

Daga bisani Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi ya sulale da mai gidan nasa gaban jami'an hukumar EFCC.

Kara karanta wannan

EFCC ta 'gano' asusun da Sambo Dasuki ya tura kudin makamai

EFCC ta janye korafinta kan Yahaya Bello

A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta janye korafi da ta shigar kan tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Hukumar ta sanar da janye daukaka kara da ta shigar kan dakatar da ita da kotu ta yi kan kama tsohon gwamnan.

EFCC ta shigar da korafin ne inda ta ke kalubalantar kotun kan matakin da ta dauka game da kama Yahaya Bello kan badakalar N84bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel