Azumi 30: Sarkin Musulmi Ya Sanar da Ranar da Za a Yi Ƙaramar Sallah a Najeriya

Azumi 30: Sarkin Musulmi Ya Sanar da Ranar da Za a Yi Ƙaramar Sallah a Najeriya

  • Fadar mai martaba Sarkin Musulmi ta sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Ƙaramar Sallah ba a faɗin Najeriya ranar Litinin
  • Bisa haka ta bayyana ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, 2024 a matsayin ranar da Musulmai za su yi Ƙaramar Sallah
  • Hakan na nufin za a tashi da azumin ranar Talata domin cika 30 kamar yadda addinin musulunci ya tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Mai alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad na III, ya ayyana ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, 2024 a matsayin ranar da za a yi Sallah Ƙarama.

Sarkin Musulmin ya bayyana cewa hakan ya biyo bayan rashin ganin jinjirin watan Shawwal a faɗin Najeriya ranar Litinin, 29 ga watan Ramadan. 1445AH.

Kara karanta wannan

Bayan gama duban wata, Saudiyya ta sanar da ranar idin ƙaramar sallah a 1445/2024

Sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar.
Fadar Sarkin Musulmi ta ce ba a ga watan Shawwal ba a Najeriya Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Facebook

Sultan wanda shi ne shugaban majalisar ƙoli ta harkokin Musulunci a Najeriya ya tabbatar da haka ne a wata sanarwa da kwamitin duban wata ya wallafa a manhajar X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin kula da harkokin Musulunci na fadar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Junaidu, ta ce ba a ga watan Shawwal ba.

Ta ce fadar Sarkin Musulmi ta amince da rahotanni rashin ganin watan kuma ta ayyana ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu a matsayin ranar 1 ga watan Ƙaramar Sallah.

Sultan ya tura saƙo ga ƴan Najeriya

"Mai alfarma Sarkin Musulmi na taya ɗaukacin al'ummar Musulmai barka da Sallah tare da fatan Allah ya ƙara tabbatar da su a kan tafarkin shiriya.
"Sultan ya kuma roƙi musulmai su ci gaba da addu'ar neman zama lafiya kana ya taya su murnar zuwan idin Karamar Sallah (Eid-El-Fitri)."

Kara karanta wannan

Saudiyya ta bayyana ranar karamar sallah bayan samun rahoton kwamitin ganin wata

- Cewar sanarwar.

Saudiyya ta fitar da sanarwa

Wannan na zuwa ne awanni bayan ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba, za a ci gaba da azumi ranar Talata.

Har ila yau, ta kara da cewa za a gudanar da Sallar Eid-El-Fitr ne a ranar Laraba 10 ga watan Afrilu bayan cika azumi 30.

Sheikh Idris ya koma Bauchi

A wani rahoton kuma Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya samu tarba daga magoya bayansa, inda suka taro shi daga bayan gari har zuwa kofar gidansa.

Dalibansa sun ce malamin ya samu gagarumar nasara cikin wata hijira da ya yi ta tsawon makonni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel