Saudiyya Ta Bayyana Ranar Karamar Sallah Bayan Samun Rahoton Kwamitin Ganin Wata
- Hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa ba a ga watan Shawwal ba bayan tawagar masu duba wata ba su ga watan a yau ba
- Wannan na nufin a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu za a gudanar da Sallah karama a Saudiyya
- Har yanzu ana dakon sakamakon ganin Shawwal a ranar Litinin, wanda fadar sarkin Musulmi ta ce za ta bayyana Talata a matsayin ranar Sallah idan an ga wata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Saudiyya - Hukumomin Saudiyya sun bayyana ranar Laraba a matsayin ranar sallah ƙarama.
A shafinta na haramain a X, tawagar ganin wata ba su ga watan Shawwal ba.
Wannan na zuwa ne sakamakon gaza ganin jaririn watan Shawwal da tawagar duban wata su ka yi a Litinin ɗin nan.
Rashin ganin watan na nufin sallah ƙarama za ta kama ranar 10 ga watan Afrilu.
![Hukumomin Saudiyya sun bayyana ranar Sallah Hukumomin Saudiyya sun bayyana ranar Sallah](https://cdn.legit.ng/images/1120/6363533e72ac8597.jpeg?v=1)
Asali: Twitter
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ranar Larabar za ta zamo 1 ga watan Shawwal 1445A.H sannan kuma ana da labari an fara duban watan Shawwal a Najeriya
Sakamakon duba watan Sallah a Najeriya
Fadar Sarkin Musulmi ta umarci Musulman Najeriya su ci gaba da duban watan karamar Sallah a yau.
A sanarwar da Sakataren NSCIA Farfesa Ishaq Oloyede ya fitar ranar Lahadi, za a bayyana Talata 1 ga watan Shawwal idan an ga watan.
Akasin ganin watan na nufin za a yi sallah ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu.
Yadda za a sanar da hukumomi ganin wata
Fadar mai martaba Sarkin Musulmin ta ce duk wanda ya ga watan zai iya tuntubarsu domin sanar da su.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/6363533e72ac8597.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Bayan gama duban wata, Saudiyya ta sanar da ranar idin ƙaramar sallah a 1445/2024
Ta cikin sanarwar da da fadar ta fitar, ta rubuta lambobin wayar da za a tuntube su domin sanar da ganin watan.
Yau Kwanaki 29 da fara azumi a duniya
A ranar 11 ga watan watan Maris ne Musulmin duniya suka ɗauki azumin watan Ramadan.
Yau Kwanaki 29 ke nan da fara azumin a sassan duniya daban-daban.
A kasashe irinsu Saudiyya, za su yi azumi 30 saboda rashin ganin watan Shawwal a ranar Litinin.
Asali: Legit.ng