Ramadan 2024: Sarkin Musulmi Ya Sanar da Ranar da Ake Kyautata Zaton Za a Yi Karamar Sallar Bana

Ramadan 2024: Sarkin Musulmi Ya Sanar da Ranar da Ake Kyautata Zaton Za a Yi Karamar Sallar Bana

  • Fadar Sarkin Musulmi ta sanar da ranar da ya kamata Musulmai a Najeriya su fara duban watan Shawwal na 1445H
  • Musulmai na ci gaba da azumtar watan Ramadana, kwanaki kadan suka rage a yi bankwana da watan mai alfarma
  • Ranar 8 ga watan Afrilu za ta kasance ranar 29 ga watan Ramadana, za a fara duban watan karamar sallah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Sokoto - Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Mai Martaba Muhammad Abubakar, ya bukaci al’ummar Musulmi da su fara duban jinjirin watan Shawwal 1445AH daga ranar Litinin 8 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Eid-el-Fitr: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranaku 2 na hutun Sallah

Sarkin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban sakataren NSCIA, Farfesa Ishaq Oloyede ya fitar ranar Lahadi, kamar yadda wakilin Legit Hausa ya gani.

Oloyede ya ce idan aka ga wata a ranar Litinin, Sarkin Musulmi zai bayyana Talata a matsayin 1 ga Shawwal da kuma ranar karamar sallah.

Za a fara duban watan sallah ranar Litinin
Sarkin Musulmi ya sanar da lokacin da za a fara duban wata | Hoto: Aliyu Magatakarda Wamakko
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lissafin ganin wata yake a bana

Sai dai ya ce idan ba a ga jinjirin watan a wannan ranar ba, Laraba 10 ga Afrilu, 2024 za ta zama ranar karamar sallar.

Wannan yana kunshe ne a cikin wani sakon da NTA ta yada a ranar Lahadi, 7 ga Afrilu a shafin Twitter.

Rubutun ya ce:

“Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci al’ummar Musulmi da su fara duban jinjirin watan Shawwal 1445AH a ranar Litinin 8 ga Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ɗan Majalisar dokokin jihar Kano ya kwanta dama da shekaru 59

"Sanarwar mai dauke da sa hannun Farfesa Sambo Wali Junaidu, shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini a Majalisar Sarkin Musulmi ta ce ranar Litinin ne 29 ga watan Ramadan 1445H kuma ranar za a fara neman jinjirin watan Shawwal."

Waye za a tuntuba game da ganin wata?

A cikin sakon, an bayyana wasu lambobin waya da za a iya tuntubar hukumar idan an ga watan a wani yanki na Najeriya.

Watan Ramadan mai alfarma zai kasance rana ta 29 a ranar Litinin, kuma da dama cikin Musulmi sun fara zuba idon ganin watan a ranar Litinin.

Karamar sallah dai biki ne da Musulmai ke yi don bankwana da watan da aka fi ayyukan ibada a cikin watannin Islama 12.

Yadda aka fara azumin Ramadana a 2024

Idan baku manta ba, an fara azumin watan Ramadana a 2024 ne a ranar 11 ga watan Maris da ta gabata.

Kara karanta wannan

Karin kudin wuta: Kano da sauran jihohi 12 da suka shirya inganta wuta ga al'ummarsu

Wannan na nufin, an shafe kusan wata guda ana azumi a jere a kasashe daban-daban na duniya, ciki har da Najeriya.

Wani rahoton Legit ya bayyana kasashen da za a fi yin azumi mai tsawo a wannan shekarar ta 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel