'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Mummunan Hari a Yobe, Sun Hallaka Soja

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Mummunan Hari a Yobe, Sun Hallaka Soja

  • Wata majiyar ‘yan sanda a Yobe ta bayyana cewa wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun lalata motocin sintiri na sojoji a jihar
  • An ce maharan sun kona motocin ne bayan hallaka wani jami’in sojan Najeriya a harin na ranar Asabar
  • Legit.ng ta ruwaito cewa tun a shekarar 2009 ake fama da tashe-tashen hankula a Arewacin Najeriya, an kashe mutane da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Yobe - Wasu ‘yan ta’adda da ake fargabar ‘yan Boko Haram ne sun kai hari a wani sansanin soji da ke garin Gujba da ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutane suna tsaka da Sallar Asham a watan Ramadana a Katsina

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito a ranar Lahadi, 24 ga watan Maris, maharan sun kashe wani jami’in soji tare da lalata motocin sintiri na sojoji a jihar.

An kashe soja a Yobe
Boko Haram sun farmaki sojoji a Yobe | Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta kuma yi nuni da cewa, ‘yan ta’addan da ake zargin sun shiga garin Gujba ne suka far wa motocin sintiri na sojoji inda suka yi artabu da jami’an tsaro a sansanin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka kai harin?

Hakazalika, an bayyana cewa, sun kai harin ne da tsakar daren ranar Asabar, 23 ga watan Maris na 2024.

Wani mazaunin garin mai Bakura Mohamed ya ce:

“Maharani ba su kashe kowa ba, ba su kuma yi sata a kantin sayar da abinci ba.
"Sun kai wa motocin sintirin biyu hari ne kawai a wani sansanin soji da ke cikin yankin."

Shugaban ‘yan sanda ya tabbatar da harin a Yobe

Kara karanta wannan

Kasashen Spain, Ireland, Malta, Slovenia sun amince su yi aiki wajen 'yantar da Falasdinu

Hakazalika, jami'in 'yan sanda yankin Gujba ya tabbatar da aukuwar mummunan harin da ya kai ga barna ga sojoji.

Sai dai ya kara da ba da haske da cewa:

“Kawo yanzu ba a samu asarar rayukan ba, ina sane da cewa motocin jami’an tsaro guda biyu sun kone gaba daya sannan soja daya ya mutu.”

An kashe masallata a jihar Katsina

A wani labarin, wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai hari gidan wani mutum, inda suka hallaka shi tare da sace ahalinsa.

An ruwaito cewa, sun kashe mutumin ne a lokacin da yake sallar Tarawih tare da ahalinsa a jihar Katsina

Jihar Katsina na daga jihohin da 'yan bindiga ke cin karensu ba babbaka a Arewacin Najeriya a 'yan kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel