'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Arewa, Sun Sace Gomman Mutane

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Arewa, Sun Sace Gomman Mutane

  • Aƙalla mutum 16 da suka haɗa da yara da mata aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kogo da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina
  • Harin ya haifar da tashin hankali a tsakanin mazauna ƙauyen dangane da halin da ake ciki na tsaro
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, bai dawo da sar saƙon da aka tura masa ba kan aukuwar lamarin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Faskari, jihar Katsina - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane 16 da suka haɗa da yara, da mata a ƙauyen Kogo da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina.

A cewar Vanguard, wani mazaunin garin ya ce ƴan bindigan sun kai hari ƙauyen ne da misalin ƙarfe 8:20 na ranar Alhamis 8 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sama da 100 sun kai hari a jihar Arewa, sun halaka mutane masu yawa

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
'Yan bindiga sun sace mutum 16 a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

An tattaro cewa an shammaci mutanen ƙauyen ne yayin da maharan suka aiwatar da mugun shirin nasu cikin ƙwarewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maharan sun shiga cikin jama'ar ne cikin nutsuwa, inda suka ajiye baburansu daga nesa don gudun kada a ganosu, rahoton Daily Post ya tabbatar.

A cewar majiyar:

"Ba tare da haifar da hayaniya ba, maharan sun kai hari wani gida inda daga bisani suka tafi da mutun16 da suka haɗa da yara, mata da maza."

An shiga tashin hankali a cikin ƙauyen yayin da mazauna ƙauyukan ke cikin fargaba suna jiran samun bayanai kan halin da ake ciki.

Majiyar ta ce mazauna yankin sun damu matuka game da lafiyar waɗanda aka yi garkuwa da su.

Me hukumomi suka ce kan harin?

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq domin samun ƙarin bayani kan harin, da ƙokarin da jami'an ƴan sanda ke yi kan lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai sabon hari a Yobe, sun halaka dan sanda da wasu mutum 2

Sai dai, kakakin rundunar ƴan sandan bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta wayarsa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari a Kogi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a ƙaramar hukumar Omala ta jihar Kogi.

Ƴan bindigan a harin da suka kai a ƙauyen Agojeju-Odo na ƙaramar hukumar, sun halaka mutum huɗu da ba su ji ba, ba su gani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel