Sojoji sun halaka yan bindiga 58, sun ceto mutane 75 daga hannunsu a Zamfara

Sojoji sun halaka yan bindiga 58, sun ceto mutane 75 daga hannunsu a Zamfara

Dakarun rundunar Sojojin Najeriya dake aikin tabbatar da tsaro a jahar Zamfara a karkashin inuwar ‘Operation sharan daji’ sun samu nasarar halaka wasu yan bindiga da dama a wasu karanbatta da suka yi da juna a dazukan Dumburum da Gando na jahar Zamfara.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jami’in watsa labaru na Operation sharan daji, Manjo Clemente Abiade ne ya bayyana haka a ranar Laraba 23 ga watan Janairu a garin Sakkwato, inda yace Sojoji sun kashe yan bindiga guda hamsin da takwas.

KU KARANTA: Rundunar Sojojin Najeriya ta bullo da sabon tsarin yaki da miyagun mutane a Kaduna

Sojoji sun halaka yan bindiga 58, sun ceto mutane 75 daga hannunsu a Zamfara
Motarsu
Asali: Facebook

Manjo Abiade yace Sojojin sun kashe yan bindigan ne a yayin wata arangama da suka yi a ranar 20 ga watan Janairu a a dajin Dumburum da kuma dajin Gando, inda suka tarar da yan bindigan dauke da muggan makamai suna shirin fita aiki.

Baya ga yan bindigan da suka halaka a sakamakon artabun, wasu da dama sun ranta ana kare a sanadiyyar fin karfi da Sojojin suka nuna musu, sa’annan sun kwato makamai da dama da suka hada da bindigu guda shirin da babura 40.

“Kidayan da mukayi bayan artabun ya nuna mun kashe yan bindiga guda 58, yayin da muka kama guda daya, mun lalata sansanonin yan bindiga guda 18, tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa dasu guda 75 wadanda yawancinsu yan kauyukan jahar Zamfara ne.

Sojoji sun halaka yan bindiga 58, sun ceto mutane 75 daga hannunsu a Zamfara
Motarsu
Asali: UGC

“Sai dai Sojoji guda biyu, tare da Sojojin sa kai na Civilian JTF guda biyu sun rasa rayukansu a sanadiyyar arangamar, haka zalika Sojoji guda takwas da Sojojin sa kai shida sun samu rauni, wanda a yanzu haka sun samun kulawa a cibiyar kula da lafiya dake Gusau.

“Tuni muka sanar da iyalan wadanda suka mutu daga cikin Sojoji, yayin da aka yi jana’izar yan Civilian JTF a karamar hukumar Anka kamar yadda dokokin addinin musulunci suka tanadar.” Inji shi.

Daga karshe kaakakin yace babban kwamandan Operation sharan daji, Manjo Janar S.O Olabanji ya mika ta’ziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasu, sa’annan ya jaddada manufarsa ta kawo karshen ayyukan yan bindiga a jahar Zamfara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel