Na shirya tsaf domin kare kaina daga zargin satar kudin makamai – Sambo Dasuki

Na shirya tsaf domin kare kaina daga zargin satar kudin makamai – Sambo Dasuki

Jim kadan bayan fitowarsa daga hannun hukumar DSS, mashawarcin tsohon shugaban kasa Jonathan a kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki ya bayyana cewa a shirye yake ya fara kare kansa a gaban kotu.

Gwamnati na zargin Dasuki da laifin mallakar miyagun makamai ba tare da ka’ida ba, tare da hannu cikin badakalar kudi naira biliyan 35 da kuma satar kudin makamai dala biliyan 2.1 da aka ware domin sayen makamai.

KU KARANTA: Mutane 2 sun mutu a harin da yan bindiga suka kai garuruwan jahar Kebbi

Dasuki ya tabbatar da komawa kotu ne cikin wata hira da yayi da gidan rediyon BBC Hausa inda yace: "Zan cigaba da gurfana gaban kotu, daman a daina zuwa kotun ne saboda kotu ta bada beli na, amma gwamnati bata da niyyar saki na, amma tunda sun sake ni yanzu, zan koma”

Dasuki ya sake nanata ra’ayinsa na cewa bas hi da rigima da wani ko wata, ba kamar yadda jama’a ke yayatawa ba, inda wasu ke ganin wai akwai jikakkiyar takun saka tsakaninsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari tun zamanin mulkin Soja.

A cewarsa, duk abin da ya samu mutum toh haka Allah Ya tsara masa, don haka shi ya yi Imani haka Allah Ya kaddara masa, saboda haka a cewarsa rashin Imani ke sanya wasu mutane su dinga danganta ibtila’in da ya shiga ga wani mutumi.

Daga karshe ya tabbatar da cewa babu wata matsala dake damunsa game da lafiyarsa ko wani abu makamancin haka, sa’annan ya kara da cewa ya tarar da iyalansa cikin koshin lafiya. “Alhamdulillahi kowa na nan lafiya.” Inji shi.

A wani labari kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gogaggen dan siyasa, kuma kwararre wanda ke yi ma jam’iyya bauta.

Buhari yace: “Ganduje kwararren dan siyasa ne daya taimaka wajen gina jam’iyyar APC, tare da aiki tukuru wajen samun nasarar jami’yyar. Gwamnan Kano na daga cikin yan siyasa masu hakuri kuma masu lissafi da na taba gani a rayuwata”.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel