Kwankwaso Da ’Yan Kwankwasiyya Sun Ci Amanata, Wanda Ya Kafa NNPP Ya Fame Tsohon ’Yambo

Kwankwaso Da ’Yan Kwankwasiyya Sun Ci Amanata, Wanda Ya Kafa NNPP Ya Fame Tsohon ’Yambo

  • Mutumin da ya kafa jam’iyyar NNPP ya bayyana yadda Kwankwaso da ‘yan Kwankwasiyya suka yaudare shi bayan zabe
  • A cewarsa, ya taimakawa Kwankwaso ne ya ba shi damar yin takara a jam’iyyar, inda yace shi ke da iko a kanta har yanzu
  • Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin ‘yan Kwankwasiyya da wasu daga tsagin ‘yan NNPP a Najeriya saboda wasu dalilai

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Najeriya - Mu’assasin jam’iyyar NNPP, Dr Boniface Aniebonam, ya ce yunkurin da Sanata Rabi’u Kwankwaso da yan Kwankwasiyya na sace jam’iyyar daga hannunsa cin amana ne.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wani taron manema labarai a Legas ranar Juma’a, inda ya ce ya bai wa Kwankwaso dama a NNPP ne domin ya cimma burinsa na siyasa na zama shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Rikicin gida: Matashi ya bar PDP saboda gaza ladabtar da mutum 2 da suka ci amana

Kwankwaso ya ci amanata, inji wanda ya kafa NNPP
Wanda ya kafa NNPP ya zargi Kwankwaso da cin amanarsa | Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Asali: Facebook

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ya shiga wannan jam’iyyar ne saboda dalili guda daya na cewa ya so ya zama shugaban Najeriya a zaben 2023 da ya gabata.”

Waye ya yiwa NNPP rajista a tun farko?

Ya yi nuni da cewa, shi kadai ya yi rajista tare da renon NNPP daga shekarar 2002 har zuwa 2022 lokacin da Kwankwaso da tawagarsa suka tunkare shi domin ya daga tutar jam’iyyar a zaben 2023, rahoton jaridar Leadership.

Ya kara da cewa:

“Buba Galadima ne ya jagoranci wata tawaga da ta hada da Sanata Suleiman Hunkuyi da Farfesa Sam Angai zuwa gida na a Anambra domin rokon mu karbi Kwankwaso a NNPP.
“Bayan tattaunawar, na kira Kwankwaso a waya, bayan kuma na yi masa tambayoyi kan manufarsa ga Najeriya, sai na ba shi tutar jam’iyyar NNPP a matsayin dan takararta shi kadai."

Kara karanta wannan

Taron NEC: Babban jigo ya buƙaci shugaban PDP na ƙasa ya yi murabus nan take

Yadda Kwankwaso ya ci amana ta, mu’assasin NNPP

A cewarsa, ya dauki nauyin tafiyar nnpp shekaru 22 kuma Kwankwaso ya so ya sace ta duk da ba dan kwamitin amintattu ba ne ko kuma shugaban jam’iyyar.

Dokta Aniebonam ya bayyana cewa ya kafa NNPP ne bayan ya kafa kungiyar NAGAFF, don haka NAGAFF ita ce uwar jam’iyyar NNPP, Daily Sun ta tattaro.

Ya tuna cewa an kori Kwankwaso da wasu daga jam’iyyar ne saboda wasu abubuwan da suka aikata na saba wa jam’iyyar amma a matsayinsa na jigon jam’iyyar mai madafun iko zai yafewa Kwankwaso idan ya wanke kansa daga abin da ya faru.

NNPP ta dakatar da Abba Kabir Yusuf?

A wani labarin, kwamitin gudanarwar NNPP ta a matakin kasa ya musanta dakatar da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Kwamitin ya bayyana cewa babu wani dalili da zai sa a dakatar gwamnan daga jam'iyar NNPP, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Idan ba ku manta ba a ranar Talata, tsagin NNPP karkashin jagoranci Major Agbor ya sanar da dakatar da gwamnan Kano na tsawon watanni shida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel