Ramadan 2024: Hukumomin Saudiyya Sun Sanar da Ganin Jaririn Watan Ramadana

Ramadan 2024: Hukumomin Saudiyya Sun Sanar da Ganin Jaririn Watan Ramadana

  • Daga karshe dai hukumomin Saudiyya sun bayyana ganin jaririn watan Ramadana na hijira 1445 daidai da 2024
  • Wannan na zuwa ne bayan shafe lokaci ana aikin hange a sararin samaniya, kamar yadda hukumar ta fadi
  • A Najeriya, 'yan kasar na ci gaba da zuba ido ko za su ga watan, kafin daga bisani su dauki Azumin bana

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Sudair, Saudiyya - Hukumomin kasar Saudiyya sun sanar da za a fara yin Azumin watan Ramadana daga ranar 11 ga watan Maris na 2024.

Wannan na zuwa ne bayan da aka ga jaririn watan na Ramadana da yammacin yau Lahadi, 10 ga watan Maris, daidai da 29 ga watan Sha'aban 1445.

Kara karanta wannan

Ramadan 2024: Muslman Najeriya na zuba ido kan ganin jaririn watan Ramadana

Ana sa ran, al'ummar musulmi a duniya za su fara Azumin na Ramadana, watan da kowa ke maida hankali ibada da neman kusanci ga Allah.

Kasar Saudiyya ta sanar da ganin watan Ramadana
An ga watan Ramadana a Saudiyya | Hoto: Inside the Haramain
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da hukumar ta sanar

A sanarwar da Inside the Haramain ta fitar, tuni aka fara shirye-shiryen fara ayyukan ibadun watan na Ramadana.

Sanarwar ta ce:

"An ga watan Ramadan na hijira 1445 a kasar Saudiyya a yau, gobe za ta kasance 1 ga watan Ramadana, wato daidai da 11 ga watan Maris 2024."

Al'ummar Musulmi na murnar shiga Ramadana

A kasan sanarwar, al'ummar Musulmi da dama sun bayyana martaninsu da ganin watan na Ramadana, inda wasu ke cewa:

Naziru Abubakar:

"Masha Allah, Allah ya bamu albarkar wannan wata Mai albarkah."

Parwiz Khan Karokhail:

"Ina taya 'yan uwa Musulmi maza da mata a fadin duniya shigowar watan Ramadana. Allah ya muku albarka."

Kara karanta wannan

Ramadan 2024: Jerin kasashen da musulmai za su yi azumi mafi tsawo da gajarta

Sadauki Jibia:

"Cikin ikon Allah da amincewarsa an samu ganin jinjirin watan Ramadan a kasar Saudi Arabia , muna fatan Allah yasa mu fara Azumi lafiya mu gama lafiya."

Anas Barde:

"AlhamdulilLah. Allah Ya sadamu da alherin dake cikin watan."

Ana ci gaba da zuba ido a Najeriya

A bangare guda, al’ummar Najeriya da sauran kasashen duniya na ci gaba da zuba ido kan ganin watan Ramadana domin fara ibada mafi girma a wurin Musulmai.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da shiri da sanya ido a kasar domin samun rahotannin da ke bayyana ganin watan ko akasin hakan.

A lissafin wata, yau ne 29 ga watan Sha’aban, wacce ke zuwa gabanin Ramadana da ake Azumin kwanaki 29 ko 30.

Asali: Legit.ng

Online view pixel