Yanzu Yanzu: Ba a Ga Jinjirin Watan Ramadana Ba a Kasar Saudiyya, Alhamis Take Azumi

Yanzu Yanzu: Ba a Ga Jinjirin Watan Ramadana Ba a Kasar Saudiyya, Alhamis Take Azumi

  • Kwamitin neman wata na kasar Saudiyya ya sanar da rashin ganin jinjirin watan Ramadana a kasar
  • A ranar Alhamis, 23 ga watan Maris ne daukacin al'ummar Musulmi za su tashi da azumin watan Ramadana
  • Watan Sha’aban na Hijira 1444 zai cika kwanaki 30 kamar yadda mahukunta na masallacin Harami suka sanar

Rahotanni da ke zuwa mana yanzu daga kasar Saudiyya shine cewa ba a ga jinjirin watan Ramadana ba a yammacin yau Talata, 21 ga watan Maris.

Kwamitin neman wata na Hilal karkashin jagorancin Dr. Abdullah Khudairi basu ga watan Ramadana na Hijira 1444 ba a yammacin Talata.

Hoton masallaci da tambarin wata
Yanzu Yanzu: Ba a Ga Jinjirin Watan Ramadana Ba a Kasar Saudiyya, Alhamis Take Azumi Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Shafin masallacin harami ya rahoto cewa kwamitin wanda ke zaune a Tumair, birnin Riyadh, da sauran yankuna suma basu bayar da rahoton ganin jinjirin watan ba.

Jami’an kotun masarautar sun aika da irin wannan hukuncin zuwa kotun kolin kasar Saudiyya domin sanar da al’ummar kasar da ma duniya labarin sakamakon binciken neman jinjirin watan na yau.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Zamfara Ta Sanya Dokar Hana Fita Daga Wayewar Gari Zuwa Dare

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Za a fara sallar Tarawee daren ranar Laraba

Bayan haka, watan Sha’aban na Hijira 1444 zai cika kwanaki 30, sannan watan Ramadan 1444 zai fara a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris 2023.

Kamar yadda safin Haramain SHarifain ya wallafa, za a fara sallar Taraweeh a masallatai masu tsarki biyu bayan sallar Ishai daga ranar Laraba, 22 ga watan Maris.

Najeriya: Sarkin Musulmi ya ce Musulmai su fara neman wata ranar Laraba

A gefe guda, mai alfarma sarkin Musulmi na Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bukaci daukacin al'ummar Musulmi a kasar da su fara neman jinjirin watan Ramadan a yammacin ranar Laraba, 22 ga watan Maris.

Sultan wanda shine Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya fadi hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakin kwamitin NSCIA, Arc. Zubairu Haruna Usman Ugwu, ya fitar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Naɗa Mutane 7 a Manyan Mukamai, Ya Aike da Sako Majalisar Dattawa

Ya kuma yi kira ga Musulman Najeriya da su mayar da hankali wajen yi wa kasar addu'o'i na musamman a cikin wannan wata mai tsarki.

Hakazalika ya yi kira ga masu wadata da su yi kokari wajen taimakawa talakawa da gajiyayyu da sadaka a cikin wannan wata na azumi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel