'Yan Bindiga Sama da 100 Sun Kai Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Mutane Masu Yawa

'Yan Bindiga Sama da 100 Sun Kai Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Mutane Masu Yawa

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun saƙwantar da ran mutum huɗu a wani harin ta'addanci da suka kai a ƙauyen Agojej-Odo na jihar Kogi
  • Da yake tabbatar da aukuwar harin, wani ɗan majalisar dokokin jihar ya bayyana cewa ƴan bindiga sama da 100 ne suka kai hari a ƙauyen
  • Ya miƙa ƙoƙon bararsa ga gwamnan jihar da ya sanya kwamishinan ƴan sandan jihar ya tura jami'ansa zuwa ƙauyen domin kare rayuka da dukiyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Rahotanni sun ce an kashe mutum huɗu bayan wani hari da wasu ƴan bindiga suka kai kan mutanen ƙauyen Agojeju-Odo da ke ƙaramar hukumar Omala ta jihar Kogi.

Jaridar Daily Trust ta ce wani ɗan majalisar dokokin jihar Kogi, Umar Yahaya ya tabbatar da kisan a jiya yayin da yake zantawa da manema labarai bayan miƙa rahoton harin ga gwamnan jihar Kogi, Usman Ahmed Ododo.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai sabon hari a Yobe, sun halaka dan sanda da wasu mutum 2

'Yan bindiga sun halaka mutum hudu a Kogi
'Yan bindiga sun kai hari a Kogi Hoto: Ahmed Usman Ododo
Asali: Twitter

Ƴan bindiga sama da 100 suka kai harin

Ɗan majalisar wanda ke wakiltar mazaɓar Omala a majalisar, ya yi iƙirarin cewa sama da ƴan bindiga 100 ne suka mamaye ƙauyen domin ƙaddamar da harin a ranar 30 ga watan Janairun 2024 da misalin ƙarfe 3:30 na rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ƴan bindigar sun shiga cikin ƙauyen ne ta gabashin garin da ke iyaka da jihohin Nasarawa da Benue, inda suka yi harbi kan mai uwa da wabi, rahoton Kogi Reports ya tabbatar.

Sai dai, ɗan majalisar ya roƙi gwamnatin jihar da ta sanya kwamishinan ƴan sandan jihar Kogi, Benthrand Onuoha da sauran shugabannin hukumomin tsaro, da su tura jami’ansu zuwa yankunan da abin ya shafa domin tabbatar da doka da oda.

Ƴan Bindiga Sun Halaka Basarake a Kogi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun halaka wani mai sarautar gargajiya a jihar Kogi a wani sabon hari.

Miyagun ƴan bindigan a yayin harin da suka kai, sun halaka basaraken mao riƙe da sarautar Elepe na Ohi-Ogidi, Cif Olayinka Ojo a ƙaramar hukumar Ijumu da ke jihar ta Kogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel