'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Sabon Hari a Yobe, Sun Halaka Dan Sanda da Wasu Mutum 2

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Sabon Hari a Yobe, Sun Halaka Dan Sanda da Wasu Mutum 2

  • Ƴan ta'addan Boko Haram ɗauke da makamai sun tafka sabuwar ta'asa a jihar Yobe a wani sabon harin da suka kai
  • A sabon harin da suka kai a garin Kukareta na ƙaramar hukumar Damaturu ta jihar sun halaka mutum uku ciki har da wani jami'in ɗan sanda
  • Ƴan ta'addan sun kuma yi awon gaba da motar rundunar haɗin gwiwa ta fararen hula a yayin harin na su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai wani sabon hari a jihar Yobe inda suka halaka mutum uku, ciki har da wani sufeton ƴan sanda.

Harin an kai shi ne a garin Kukareta da ke ƙaramar hukumar Damaturu ta jihar, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke rikakken dan bindiga a Kano, bayanai sun fito

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai sabon hari a Yobe
'Yan ta'addan Boko Haram sun halaka mutum uku a Yobe Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

An tattaro cewa ƴan ta’addan sun ƙona jami’in ɗan sandan tare da wani wurin kwana na wucin gadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun kuma kwashe makamai da alburusai a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Ƴan ta'adda Boko Haram sun tafka ɓarna

Sun kuma harbe wasu fararen hula biyu tare da ƙona motar hakimin garin tare da yin awon gaba da wata motar ƙirar Hilux guda ɗaya ta rundunar haɗin gwiwa ta fararen hula da ke aiki a garin, rahoton New Telegraph ya tabbatar.

A cewar wata majiya daga cikin jami’an tsaro, motar kwamandan sashe na biyu na rundunar Operation Hadin Kai, a yayin ziyara wajen da lamarin ya faru, ta taka wani bam da aka dasa a kan hanya.

Bam ɗin ya lalata motar kwamandan tare da raunata direbansa a ƙafa yayin da kwamandan da mai kula masa da rediyonsa ba su ji rauni ba.

Kara karanta wannan

Ana cikin halin matsi a Najeriya, Remi Tinubu ta fadi lokacin da sauki zai zo

Harin na baya-bayan nan na zuwa ne kwanaki biyar bayan wani harin makamancin irin wannan, ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an ƴan sanda huɗu a Gajiram, hedkwatar ƙaramar hukumar Nganzai ta jihar Borno.

Ƴan Ta'adda Sun Dasa Bam a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani bam da ƴan ta'addan Boko Haram suka dasa a kan hanya ya salwantar da rayukan mutum 12.

Mutanen dai suna cikin tafiya ne a lokacin da motarsu ta taka bam ɗin a hanyar Pulka zuwa Gwoza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel