Tashin Hankali Yayin da Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Bacci da Mahaifiyarta a Jihar Arewa

Tashin Hankali Yayin da Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Bacci da Mahaifiyarta a Jihar Arewa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Rikici ya barke tsakanin wasu iyali a jihar Nasarawa sakamakon ikirarin da wata matar aure ta yi cewa mijinta ya ci amanarta ta hanyar kwanciya da mahaifiyarta.

Matar mai suna Doris ta ce danta mai shekaru shida ne ya tona asirin mijin nata mai shekaru 46 da mahaifiyarta, rahoton The Nation.

Matar aure na zargin mijinta da neman mahaifiyarta
An yi amfani da hoton don misali ne Hoto: Delmaine Donson
Asali: Getty Images

"Yana gamsar dani sosai", uwar matar

Abin mamaki, mahaifiyar Doris, Madam Cynthia, ba ta musanta zargin soyayyar dake tsakaninta da surukinta ba lokacin da 'yarta ta tunkareta da zargin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maimakon haka, ta gaya wa ’yarta cewa akwai dangantaka tsakaninta da surukinta (mijin ’yarta), Joseph, kafin su yi aure, kuma shi ne damar da ta samu na yin soyayya mai dadi shekaru 20 bayan mutuwar mijinta.

Kara karanta wannan

Yadda masu garkuwa da mutane suka kashe shugaban makarantar Kaduna, ya bar mata 3 da yara 13

Madam Cynthia ta ce:

"Mijina ya mutu shekaru 20 da suka wuce, kuma ban taba samun wani namiji da nake mafarkin samu ba sai da na hadu da Joseph.
“Shi mutum ne mai kirki kuma mai karamci. Mutum ne mai kafi da jini a jika kuma ya iya kwanciyar aure.
"Yana gamsar dani sosai irin wanda ban taba samu daga wani namiji ba. Saboda haka, bana son rabuwa da shi, don haka na hada shi da ke (Doris)."

Yadda mahaifiyar Doris ta hada surukinta da 'yarta

Doris, mai shekaru 28 ta auri Joseph, manaja a wani kamfani mai zaman kansa, ba tare da sanin cewa shi da mahaifiyarta suna soyayya ba.

Kamar yadda abun yake, Madam Cynthia ce ta jawo hankalin Joseph ya auri diyarta (Doris), wacce a lokacin take zaune a Keffi a matsayin dalibar Jami’ar Jihar Nasarawa.

Kasancewar Doris bata ziyartan Lafia akai-akai, bata da masaniya kan yadda mahaifiyarta da mijin nata suke tarayya.

Kara karanta wannan

'Yan makarantar Ekiti: An bar yaranmu da yunwa sannan ga duka, Iyaye

An tattaro cewa Joseph da Madam Cynthia suna gudanar da abubuwansu cikin hikima ta yadda da wuya mutum ya gane akwai abin da ke wakana a tsakaninsu.

An rahoto cewa Joseph baya tashi daga ofis da wuri, inda daga bisani zai jira Madam Cynthia a gidansa na Lafia bayan ta tashi daga shagonta na siyar da abinci.

Wa ya kama surukan suna cin amana?

Asiri ya tonu ne a ranar 18 ga watan Janairu, lokacin da Madam Cynthia ta ziyarci gidan 'yarta dake Sabon Nyanyan, karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa.

An ce Joseph ya koma Nyanyan saboda ya kisanci matarsa wacce ya samawa aikin gwamnati a Abuja.

Kamar yadda suka saba a tsakaninsu, Joseph da mahaifiyarsa (Cynthia) sun yanke shawarar komawa dabi'arsu ta tarayya da juna yayin ziyarar.

Abun bakin ciki, dansu mai shekaru shida ya kama su suna aika-aika sannan daga bisani ya tona asiri, rahoton LIB.

Kara karanta wannan

"Ina cikin damuwa" Gwamnan PDP ya faɗi halin da yake ciki saboda rikicin siyasar jiharsa

Budurwa ta kama ma'aurata suna cin amanar juna

A wani labarin kuma, wata matashiya ta shiga tasku bayan ta gano sharholiyar da 'yar uwarta da mijinta suke yi a boye inda suka bata toshiyar baki.

Yayar tata ta bata naira miliyan 5 don ta boyewa mijinta sirrin inda shi kuma ya yi mata alkawarin karatu a Turai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel