‘Yan Makarantar Ekiti: An Bar Yaranmu da Yunwa Sannan Ga Duka, Iyaye

‘Yan Makarantar Ekiti: An Bar Yaranmu da Yunwa Sannan Ga Duka, Iyaye

  • Rahotanni sun kawo cewa masu garkuwa da mutanen da suka sace 'yan makaranta a jihar Ekiti suna barinsu da yunwa tare da muzguna masu
  • Iyayen yaran da suka iya hada N470,000 daga kudin fansar da aka nema, sun ce lamarin ya jefa su cikin halin wayyo Allah
  • Sai dai kuma, rundunar 'yan sanda ta ce ta baza jami'anta cikin daji don ceto yaran kuma tuni suka kama mutum takwas da ake zargi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Ekiti - Iyayen 'yan makaranta da aka yi garkuwa da su a jihar Ekiti, a ranar Alhamis, sun roki a gaggauta ceto su, suna masu cewa an bar yaran babu abinci babu wajen kwana tun da aka sace su a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da suka sace 'yan makarantar Ekiti sun yi barazanar kashe su

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa 'yan bindigar sun nemi a biya naira miliyan 100 kudin fansar daliban su biyar da ma'aikatan makarantar hudu da aka sace.

Iyayen yaran da aka sace a Ekiti sun koka
‘Yan Makarantar Ekiti: An Bar Yaranmu da Yunwa Sannan Ga Duka, Iyaye Hoto: Niogeria Police Force
Asali: Facebook

Sai dai kuma, an rahoto cewa iyayen yaran da al'ummar gari sun yi nasarar tattara N470,000 ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani uba, Mista Adebisi Jegede, wanda aka sace matarsa (malama) da dansa, ya ce lamarin ya jefa 'yan uwan daliban wadanda suka shiga mawuyacin hali cikin damuwa.

Yayin da yake kukan cewa ya damu da halin da lafiyar mutanen ke ciki, ya ce iyayen yara sun gaza hada kudin da masu garkuwa da mutanen suka bukata.

Wani uba, wanda dansa mai shekaru 15 ke cikin mutanen da aka sace, ya ce wannan ba shine karo na farko da ake sace mutane ba a garin.

Kara karanta wannan

Kaduna: Wadanda suka yi garkuwa da wata likita da mijinta sun nemi N100m, sun yi barazanar kisa

Shugaban makarantar, Mista Gabriel Adesanya, ya kuma ce masu garkuwa da mutanen na cin zarafin dalibai da ma'aikatan da ke tsare a hannunsu.

Me hukumar 'yan sanda ta ce kan lamarin?

A halin da ake ciki, rundunar 'yan sandan jihar Ekiti ta ce ta kama karin mutum takwas biyo bayan satar wasu 'yan makaranta da aka yi a Emure-Ekiti, da kisan sarakuna biyu a Ikole-Ekiti.

Kakakin 'yan sandan Ekiti, DSP Sunday Abutu, ya ce suna ta kokari domin tabbatar da ceto mutanen da aka sace da kama wadanda suka sace su.

Kan haka ne yace sun tura tawaga ta musamman daji tare da jami'an soji, Amotekun, yan banga, maharba da 'yan Agbekoya da kuma jami'an 'yan sanda a Amotekun daga jihar Ondo.

A cewar Abutu, aikin wanda aka gudanar ta dajin Emure-Eikiti, dajin Ise/Ogbese zuwa dajin Emure-Ile a jihar Ondo, ya kai ga kamun mutum takwas da ake zargi a dajin.

Kara karanta wannan

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fi ko ina yawan masu garkuwa da mutane, in ji Seun Kuti

Jerin sunayen wadanda aka kama

Wadanda ake zargin da suka shiga hannu sun hada da Yaya Sumaila, Idrisu Abubakar, Hassan Abdullahi, Abdullahi Abdullahi,

Sauran sune Haruna Abubakar, Usman Abdullahi, Haruna Sule, da wani Babusa Alhaji Lede wanda aka kama a dajin Ayedun/ Ayebode Ekiti a dajin Ikole dake jihar.

DSP Abutu ya ce ana kan gudanar da bincike kan wadanda aka kama da kuma bayanan da zai kai ga kama sauran da suka tsere.

Me aka samo a hannunsu?

Kakakin 'yan sandan ya kuma bayyana abubuwan da aka samo daga hannun miyagun a matsayin, shanu daya, adduna uku, gatari daya da kayan abinci.

Abutu ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an kama miyagun da suka tsere tare da gurfanar da su a gaban doka.

‘Yan bindiga sun yi barazanar kashe ‘yan makarantar Ekiti

A wani labarin kuma, mun ji cewa masu garkuwa da mutanen da suka sace 'yan makaranta biyar da ma'aikatan makarantar Ekiti sun yi barazanar kashe su.

'Yan uwan wadanda aka sacen sun bayyana a ranar Alhamis, 1 ga watan Fabrairu, cewa masu garkuwa da mutanen sun rage kudin fansar zuwa naira miliyan 15, rahoton Premium Times.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel