Yadda Masu Garkuwa da Mutane Suka Kashe Shugaban Makarantar Kaduna, Ya Bar Mata 3 da Yara 13

Yadda Masu Garkuwa da Mutane Suka Kashe Shugaban Makarantar Kaduna, Ya Bar Mata 3 da Yara 13

  • Wasu iyali sun rasa mahaifinsu bayan da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi tare da hallaka shi a Koriga, Kaduna
  • An tattaro cewa an yi garkuwa da mutumin ne sannan aka tsare shi tare da matarsa da karamin dansu
  • A cewar Sanata Shehu Sani, wanda ya tuna mummunan al'amarin, mutumin ya rasu ya bar matan aure uku da yara 13

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Sanata Shehu Sani ya magantu kan rashin tsaro a Najeriya da yadda abun ke shafar iyalai.

A wata hira ta musamman da jaridar Legit, tsohon dan majalisar ya bayyana yadda ‘yan fashi suka addabi jiharsa ta Kaduna, musamman a bayan gari.

Kara karanta wannan

'Yan makarantar Ekiti: An bar yaranmu da yunwa sannan ga duka, Iyaye

Shehu Sani ya magantu kan rashin tsaro
Yadda Masu Garkuwa da Mutane Suka Kashe Shugaban Makarantar Kaduna, Ya Bar Mata 3 da Yara 13 Hoto: Shehu Sani/Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

'Dan majalisar ya bada labarin yadda 'yan bindiga suka yi garkuwa da wani shugaban makaranta a daya daga cikin kananan garuruwan Kaduna tare da matarsa mai ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Sani ya bayyana cewa an kashe mutumin, inda ya bar matar tasa mai ciki, da wasu matan biyu da yara 13.

Ya ce:

"An yi garkuwa tare da kashe wani shugaban makaranta a Koriga, Kaduna, an sace matarsa mai ciki da kuma karamin dansu.
"Ya bar mata uku da yara 13."

Shehu Sani ya daura laifin rashin tsaro kan gwamnatin Buhari

Dan majalisar ya ci gaba da nuna damuwarsa yana mai cewa lamarin ya yadu daga Arewa zuwa Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas.

Tsohon dan majalisar ya yi ikirarin cewa har yanzu ana fama da cin hanci da rashawa da rashin tsaro, yana mai alakanta su da barnar da aka yi a lokacin mulkin Buhari.

Kara karanta wannan

Mai gadin makaranta a Kano ya dauki ransa a cikin aji saboda tsohuwar matarsa ta sake aure

Shehu Sani ya magantu kan mulkin Buhari

A baya mun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce hadiman da tsohon shugaban ƙasa, Muhamnadu Buhari, ya kewayen kansa da su sun illata Najeriya.

Sanata Sani ya yi iƙirarin cewa waɗanda Buhari ya aminta ya naɗa a muƙamai sun yi kashe mu raba da dukiyar baitul mali kuma sun gurgunta makomar ƙasar.

Ya bayyana haka ne ranar Laraba, 31 ga watan Janairu, 2023 a wurin tattaunawar da Legit.ng ta shirya 'Twitter Space' mai taken, "Yaƙi da rashawa ko matsalar tsaro: Mafi muhimmanci ga FG a 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel